✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farashin litar mai zai haura N1,000 kwana nan — IPMAN 

Shugaban ya ce za a ƙara farashin ne saboda dawo da harajin Naira 10 kan kowace lita da dillalan ke biya.

Ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya (IPMAN), ta bayyana cewa farashin litar mai a gidajen mai zai kai sama da Naira 1000 nan da ’yan kwanaki masu zuwa.

Shugaban IPMAN na Arewacin Najeriya, Alhaji Salisu Ten Ten ne, ya bayyana hakan.

Ya ce ƙarin farashin ya biyo bayan umarnin da hukumar NMDPRA ta bayar na dawo da harajin Naira 10 kan kowace lita da dillalan ke biya.

Ya ce, “A baya, ana shigo da man fetur daga ƙasashen waje, kuma akwai haraji na Naira 10 kan kowace lita.

“Amma tun da matatar Dangote ta fara aiki, sai aka daina shigo da mai daga waje, wanda ya sa aka dakatar da wannan haraji.”

Sai dai, a cewarsa, yanzu hukumar NMDPRA ta dawo da harajin, wanda ya ƙara yawan kuɗin da dillalan man ke biya.

Ya ƙara da cewa, “Kafin wannan ƙarin, farashin lita a defo yana kai Naira 913.

“Yanzu kuwa, an ƙara musu Naira 10 kan kowace lita, wanda ke nufin masu gidajen mai dole su ƙara farashin don su samu riba.”

Ya ce farashin mai daga defo yanzu ya kai Naira 935, kuma idan aka ƙara kuɗin lodi da dakon mai, farashin zai iya kai Naira 1,040 zuwa naira 1,050, musamman a jihohin Arewacin Najeriya.

Shugaban na IPMAN, ya ce wannan ƙarin ba shi da alaƙa da matatar Dangote, ya ce har yanzu bata ƙara farashin mai ba.

Ya ce tashin farashin ya samo asali ne daga sabuwar dokar haraji da NMDPRA ta ƙaƙabawa dillalan mai.