An wayi garin Laraba farashin litar fetur ya kai Naira 560 a gidajen mai a Kano, a wasu jihohin kuma har Naira 700.
An kuma samu samu dogayen layuka a gidajen man da Aminiya ta ziyarta a Kano, inda farashin lita ke kaiwa farawa daga Naira 350 zuwa 560.
Aminiya ta je gidan mai na AYM Shafa, inda ake sayar da lita a kan N560, gidan man Alhaji Alasan de ke Titin Gaida a Karamar Hukumar Kumbotso na sayarwa N450; A.Y. Maikifi kuma N400, maimakon N220 da aka sayar a safiyar Talata.
Platinum Oil Services, na sayarwa N380, sai B.A Bello, kuma Naira 350, a yayin da Kanawa ke bayyana damuwa kan tashin gwauron zabon man da kuma dogayen layin da ake fama da shi a gidajen mai.
- Karancin Ruwa A Kano: Abba Gida-Gida ya ayyana dokar ta baci
- Mambobinmu har yanzu na sayar da fetur kan N196 –IPMAN
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara samun karancin man da kuma dogayen layuka a sassan, bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar cewa biyan kudin tallafin mai da gwamnati ke yi ya zama tarihi a Najeriya.
Wani mazaunin Kano, B.A. Haruna Ishaq, ya bayyana damwa kan yadda gwamnatin ta shigo, inda ya ce ko a ranar Talata ya sayi lita a kan N210, amma zuwa ranar Laraba farashin ya koma N450.
Wata matar aure mai suan A’isha Aliyu, ta koka cewa wahalar man ta sa masu baburan A Daidaita Sahu sun yi kara kudi, inda yanzu kudin da take kashewa wajen kai ’ya’yanta makaranta ya karu daga N400 zuwa N550.
Aminiya ta tuntubin Shugaban Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Kasa (IPMAN), Reshen Jihar Kano, Bashir Dan-Mallam wanda ya ce za su yi taron gaggawa kan lamarin, kafin daga baya ya yi bayani.
Za mu sa kafar wando da su…
Gwamnatin Tayyya ta sha alwashin hukunta masu neman kawo cikas ga cire tallafin man fetur, a yayin da masu bumburutu suka wasa wukarsu, bayan sabon shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar cewa biyan tallafin mai ya zama tarihi.
Tun bayan furucin na Tinubu a jawabinsa na karbar rantsuwar fara aiki a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16 a ranar Linintin, wasu gidajen mai suka dakatar da aiki, aka kuma fara samun dogayen layin ababen hawa.
Tinubu dai ya jaddada goyon bayan gwamnatinsa ga matakin da gwamnati mai barin gado ta Shugaba Muhammadu Buhari ta dauka na soke biyan kudin tallafin mai da ke lakume tiriliyoyin kudade daga aljihun gwamnatin.
“Mun jinjina wa gwamnati mai barin gado game da soke biyan tallafin mai, wanda mawadata ne suka fi amfana da shi maimakon talakawa,” in ji Shugaba Tinubu.
Sa’o’i kadan bayan nan ne, tun a ranar Litin din, wasu gidajen mai suka rurrufe, wanda ya haddasa karanci da tsadar man a wasu sassan Najeriya.
Hakan ya sa farashin litar man ya yi tashin gwauron zabo zuwa Naira 700 a wasu wurare, a yayin da fasinjoji ke kokawa bisa ninka kudin mota da aka yi.
Kungiyoyin kwadago da jami’iyyun adawa dai na ganin cewa lokacin da shugaban kasar ya yi sanarwar bai dace ba.
Amma duk da haka, gwamnatin ta ce babu gudu, babu ja da baya kan cire tallafin, wanda ke lakume tiriliyoyin Naira a duk, shekara, alhali abin da talakawa ke amfana da shi a ciki bai taka kara ya karya ba.
Majalisar Wakilai ta jaddada cewa dokar kasafin kudin 2023 ba ware ko sisi ba domin biyan tallafin man, wanda gwamnatin ta bayyana a matsayin kara wa mai karfi karfi.
A yayin da gwamnatin ta lashi takobin hukunta masu neman kawo cikas ga cire tallafin, kungiyoyin dillalan mai sun yi maraba da matakin tare da cewa za su ba da hadin kai domin ganin ba a samu karancin mai ko tsadar da ta wuce misali ba.
Masu kafar ungulu sun kuka da kansu —Kungiyar Gwamnoni
Shugaban Kungiyan Gwamnonin Najeriya (NGF) kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya gargadi gidajen mai a jihar da sauran wurare kada su kuskura su jefa mutane cikin kunci a dalili kan batun cire tallafin man.
Shi ma Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ce, Gwamnatin Tarayya za ta yi maganin duk dillalin mai da ke neman fakewa da cire tallafin ya tsawwala farasahi, inda ya ce karin farashin da dogayen layin da suka biyo bayan jawabin Tinubu a matsayin zalunci.
“Zalunci ne masu gidajen mai su yi amfani da wani yanayi da bai dace ba, domin mu kasance mutane masu gaskiya idan har muna so kasar nan ta cigaba. Dole mu yi dammara domin samun rayuwa mai nagarta a nan gaba.”
Halin da aka ciki a Legas
Yawancin gidajen mai a Legas ba su bude ba ranar Talata, wadanda suka bude kuma an samu dogayen layikan ababen hawa, wanda hakan ya sa masu ababen hawa suka ninka wa fasinjoji kudi.
Wani fasinja ya kuka cewa an ninka kudin motar da da yake hawa N700 zuwa N1,500 daga Iyana Ipaja zuwa Arepo.
Wakilanmu sun gano yadda gidajen mai ke sayar da lita a kan N500 zuwa N600 kan babban titin Mile 2 zuwa Badagry.
Duk da haka, wasu manyan gidajen mai suna sayar da lita a kan N195 amma akwai dogayen layuka.
Gidajen mai na NNPC sun sayar da lita a kan N180, inda aka samu dogayen layi sosai, sai dai kum zuwa karfe 9 na safe sun dakatar da sayarwa.
Halin da aka ciki a Abuja
Aminiya ta lura ba a bude kasarin gidajen mai a Abuja ba ranar Talata a yayin da aka samu dogayen layi a wasu wadanda suka bude a yankunan Kubwa da Kado da Jabi.
a motorist wearing a long face, said: “Gidajen mai shida na je yau amma ban samu ba saboda sun ki sayarwa. Daga gidan man Shafa a Dutse na je MRS a kan titin Dutse na wuce zuwa Mainland a Dutse, har zuwa gidajen mai da ke Kado da Jahi duk ba sa sayarwa,” in ji wani wanda ya je neman mai a Abuja, mai suna Stephen Ojunta.
Mai ya kai N700 a Bayelsa
A Yenagoa, hedikwatar Jihar Bayelsa farashin litar mai ya koma N700 daga N230 a yayin da masu bumburutu ke cin karensu babu babbaka.
Wani ’yar tireda a Abeokuta, Jihar Ogun State, Misis Azeezat Adeyemi ta ce matsalar mai ta sa ta bar motarta a gida, a yayin da mazauna garin Ilori na Jihar Kwara suka koka cewa gidajen mai sun rurrufe..
Wani dain garin, Daniel, ya ce an fara samun dogayen layikan ababen hawa a yankin Odota ranar Litinin a yayin da wasu gidajen mai suka rurrufe..
Wani mazaunin garin Bauchi, Sani Umar ya soki sanawar Tinubu na soke tallafin ba tare da daukar wani mataki ba musamman a kan gidajen mai, da kuma na rage matsalar da cire tallafin zai haifar.
Biyan tallafin mai zai durkusar da Najeriya —Shettima
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce ya zama wajibi Najeriya ta soke biyan tallafin mai, tun kafin tallafin ya durkusar da kasar.
ya shaida wa ’yan jarida a Fadar Shugaban Kasa a ranar Talata cewa cewa gwamnati na da masaniyar cewa ’yan adawa za su kushe matakin cire tallafin, inda ya kara da cewa gwamnati za tunkari batun gadan-gadan, ta magance ta.
Shettima: “Shugaban kasa ya riga ya yi magana a kan wannan batu, gaskiyar ita ce, ko dai mu kawar da tallafin man ko kuma shi ya ga bayan kasar nan.
“A 2022, an kashe Dala biliyan 10 wajen biyan tallafi kan abin da kashi 90 dinsa mawadata ke amfana, su kuma talakawa wadanda su ne akasarin ’yan kasar ba su fi su amfana da kashi 10 ba.
“Za mu sanya kafar wando da duk masu nemna kawo wa matakin nan cikas.”
Muna bin gwamnati bashin N2.8trn —NNPC
Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) Mele Kyari ya sanar cewa kamfanin na bin Gwamnatin Tarayya bashin Naira tiriliyan 2.8 na kudin tallafin mai.
Kyari, wanda ya gana da Tinubu ranar Talata ya kara da cewa makudan kudaden da ake kashewa wajen biyan tallafin mai ya hana kamfanin samun isassun kudaden da gudanar da ayyukan da suka rata a wuyansa yadda ya kamata.
Ya shaida wa manema labarai a Fadar Shugaban Kasa cewa: “Daga cikin Niara tiriliyan shida da aka ware na biyan tallafin a kasafin 2022, da kuma Naira tiriliyan 3.2 da ke cikin kasafin 2023, har yanzu gwamnati ba ta ba da ko sisi ba.
“Don haka NNPC ke biya, bayan mun biya haraji da sauran hakkoki, wanda hakan ke kawo cikas wajen gudanar da ayyukanmu
“Yanzu haka muna jiran gwamnati ta biya NNPC Naira tiriliyan 2.8 da muke bin ta na kudin tallafin, don haka ba zai yiwu a ci gaba da tafiya a haka ba,” in ji shi.
Majalisa da dillalan mai sun goyi bayan jire tallafi
Majalisar Wakilai dai ta yaba wa Shugaba Tinubu bisa tabo batun janye tallafin tun a ranar da ya karbi mulki.
Da yake jawabi a zauren majalisar a ranar Talata, Honorabul Jimoh Abdulraheem Olajide, ya tunatar da takwarorinsa cewa dokar kasafin kudin 2023 da suka yi ba ta ware wa tallafin mai ko sisi ba.
Su ma Kungiyar manyan Dillalan Mai ta Kasa (MOMAN) da ta masu Daffo-Daffo (DAPPMAN), sun goyi bayan cire tallafin da Tinubu ya yi.
Sanawar da suka fitar ta yaba masa a matsayin jarumi da ke daukar matakin kariya kan abun da ke iya nakasa tattalin arzikin kasa.
Dun kuma yi kira ga gijajen mai da kada su tsawwala farashi man fetur, suna masu ba da tabbacin cewa za su yi iya kokarinsu wajen ganin ba a samu karin farashin da zai dami jama’a ba.
Sannan suka shawarci jama’a da su guji rububin sayen mai saboda fargaba, domin kada hakan ha haifar da karancinsa.
Babu bukatar fargaba —NMDPRA
Hukumar Kula da Albakatun Mai na Kasa (NMDPRA) ta bukaci ’yan Najeriya cewa kada su samu damuwa saboda sanawar Shugaba Tinubu ta janye tallafin.
Kakakin NMDPRA Kimchi Apollo ya bayyana cewa hukumar na aiki tare da NNPC da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da ba samu wani cikas ba ko karancin man, ko kuma zaluntar masu sayen mai ko fasinjoji a dalilin janye tallafin.
Jam’iyyun adawa koka
Jam’iyyar adawa ta LP da kungiyar kwadago ta TUC sun yi tir da abin da suka kira gaban kai da Shugaba Tinubu ya yi ba tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan soke tallafin ba, wanda hakan ya jefa ’yan kasa cikin kunci.
Mukaddashin kakakin LP, Obiora Ifoh, ba a kwana biyu da sanawar da Tinubu ya yi ba, amma har farashin litar man fetur ya kai N750 a wurin masu bumburutu.
“Masu motocin haya sun yi karin kudi, su kuma masu bumburutu sai cin karensu suke yi babu babbaka; Lokacin da ya yi sanarwar bai dace ba, wannan ya nuna gwamnatinsa na da aniyar jefa mutane cikin wahala.”
Don haka ya shawarci gwamnatin da ta sake tunani ta bullo da hanyar mafi dacewa ta cire tallafin ba tare da mutane sun wahala ko an samu hargitsi ba
Shi ma dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar SDP a zaben 2023, Prince Adewole Adebayo ya ce Tinubu ya yi sanawarb ba tare da kyakkyawan shiri ba, kuma lokacin bai dai ce.
Don haka ya bukaci jama’ar Najeriya su hada kansu, domin tabbatar da ganin shugabanni sun yi abin da ya dace.
Akwai bukatar bayani –Kwararre
Wani kwararre a fannin kudi da haraji daga cibiyar PricewaterhouseCoopers (PwC) ya ce akwai bukatar gwamnatin Tinubu da hukumomin da abin ya shafa su yi cikakken bayani game da abin da yake nufi da janye tallafin man.
Ya bayyana wa tashar talabijin ta Channels cewa a lokacin yakin neman zabe, Tinubu bai yi wani nuku-nuku ba wajen bayyana matsayinsa kan cire tallafin mai, kuma sanarwar da ya yi ta isa hujja cewa ya riga ya yanke shawarar soke tallafin.
Amma ya ce bai yi tunanin gwamnatin za ta yi gaban kanta wajen jire tallafin nan take ba, domin aiwatar da hakan zai dauki makonni.
A cewarsa, gwamnatin ta dauki matakin ne saboda kada ta bude kofar da matsalar za ta ci gaba kafin cire tallafin.
Gudunmmawa daga: Sagir Kano Saleh, Sunday M. Ogwu, Balarabe Alkassim, Abbas Jimoh, Dalhatu Liman, Baba Martins, Muideen Olaniyi, Seun Adeuyi ( Abuja), Abiodun Alade, Abdullateef Aliyu, Eugene Agha (Legas), Bassey Willie (Yenagoa), Raphael Ogbonnaiye (Ado-Ekiti), Iniabasi Umo (Uyo), Maryam Ahmadu-Suka (Kaduna), Peter Moses (Abeokuta), Usman A. Bello (Benin), Mumini Abdulkareem (Ilorin), Victor Edozie (Fatakwal), Hope A. Emmanuel (Makurdi), Hassan Ibrahim (Bauchi), Salim U. Ibrahim (Kano), Adenike Kaffi (Ibadan), Habibu Idris Gimba (Damaturu), Tosin Tope (Akure), Tijjani Ibrahim (Katsina), Haruna G. Yaya (Gombe) & Ali R. Ali (Dutse).