Farashin kayan miya da sauran kayayyakin gwari ya fadi a Jihar Kano a sakamakon yawaitar kayan a kasuwanni wanda manoma ke ci gaba da kai wa bayan girbin amfanin gona.
Binciken da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya yi a kasuwar Kofar Wambai da kuma Kasuwar Rimi da ke cikin kwaryar birnin Kano, ya gano cewa farashin kayan gwarin irinsu Albasa, Tumati da Tattasai ya fadi da kashi 200 cikin dari tun bayan tashin gwaron zabi da farashinsu ya yi a watannin baya.
- Gobara ta lashe Unguwanni takwas a Borno
- Hotuna: Gwamnonin da aka yi wa allurar rigakafin Coronavirus a Najeriya
- ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda biyu a Bauchi
A yanzu ana sayar da awon Albasa Naira 100 kacal sabanin Naira 250 da aka rika sayarwa, sai kuma Tumatir wanda shi ma farashin ya fadi warwas inda ake sayar da awonsa a kan Naira 100 sabanin Naira 400 da aka rika sayarwa a baya.
Hakazalika, farashin awon Tattasai da aka rika cin kasuwarsa a kan Naira 600, a yanzu farashin ya dawo Naira 150 kacal a binciken da aka gudanar a ranar Lahadin.
Wasu daga cikin ’yan kasuwar kamar wani Malam Ibrahim Dan Borno, ya alakanta faduwar farashin da yadda manoma ke ci gaba da tururuwar kawon amfanin gonakinsu da suka girba zuwa kasuwanni, lamarin da ya ce farashin na iya kara sauka kasancewar yadda manoman ke ci gaba da kawo kayan gwari kasuwanni.
Wani dan kasuwar mai suna Sabi’u Sama’ila, ya alakanta lamarin faduwar farashin a sakamakon yadda kasuwar ta cika da kayan gwarin duba da albarkar da manoman suka samu a nomansu na rani, sai dai ya ce akwai yiwuwar yanayin farashin ya sauya saboda yadda bukata a kan kayan gwarin ke ci gaba da karuwa.
A cewar wani Abubakar Danladi mai sayar da Tumatir, tilas ce ta sanya manoman ke sayar da amfanin gonakinsu domin gudun asara a yayin da suke ci gaba da fuskantar kalubalen rashin dabaru da kayan adana amfanin gona na zamani.
Yana mai cewa, “Tumatir da sauran kayan gwari ba za su ajiyu ba musamman a irin wannan lokaci na zafi wanda dole manomi ya sayar da amfani ko kuwa ya tafka asara.”
“Rashin kayayyakin adana amfanin gona na zamani yana kara sanya wa manoma su janye jiki daga noma kayan gwari,” in ji shi.
Ya yi kira da a wayar da kan manoma a kan yadda za su rika adana amfanin gonankinsu domin samun kariya ta karyewar jarinsu.
Wata mata Amina Ibrahim da kuma mutum Bello Ahmed, sun bayyana farin cikinsu a kan yadda farashin kayan gwarin ya fadi warwas inda suke fatan farashin kayan hatsi ya karye duba da yadda manoman suka albarka a bana.