✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Farashin kayan amfanin gona ya faɗi warwas a Taraba

Sai dai ana fargabar yadda ’yan kasuwa ke sare kayan na iya sa wa su tashi

Wani binciken Aminiya ya gano cewa farashin kayan amfanin gona ya faɗi warwas a kasuwannin Jihar Taraba, saboda daminar bana ta yi kyau.

Bayanai sun nuna cewa daminar ta yi harshen ne a dukkan Kananan Hukumomin Jihar guda 16.

Ya zuwa yanzu dai, tuni aka girbe kayayyaki irin su masara da shinkafa da doya da dankalin Turawa da rogo da kankana da gero da kuma wake ɗan wuri.

A sakamakon haka, farashin babban buhun masara wanda a ’yan watannin baya ya kai N60,000, yanzu bai wuce tsakanin 20,000 zuwa 28,000 a kasuwannin ba.

Kazalika, babban buhun busasshen rogo wanda a baya ake sayarwa 28,000, yanzu ya dawo 14,000.

Farashin doya da gero da shinkafa su ma sun fadi a fadin Jihar, kamar yadda binciken namu ya gano.

Jihar Taraba dai ta samu ruwan sama ba kakkautawa, lamarin da ya sa manoma suka ce shi ya taka rawa wajen harshen daminar ta bana.

Sai dai Aminiya ta gano cewa yanzu haka masu sari na can na ta sarar sabbin amfanin da yawa a Jihar.

Sai dai wasu mazauna Jihar sun bayyana fargabar cewa sarin ’yan kasuwar zai iya sa farashin ya sake tashi.

Bello Adamu, wani dan kasuwa a kasuwar Garba-Chede da ke Jihar ya ce masu sarin sun ba dillalai miliyoyin kudi suna can suna ta saye kayan a hannun manoma.

Ya ce a kusan dukkan kasuwannin hatsin Jihar, dillalan sun gina manyan rumbuna da suke ajiye kayan amfanin gonar.

Bello ya ce ’yan kasuwar sun fi manoman samun kudi, inda ko a kakar bara sun sayi masara a kan Naira 17,000, amma sai da ta kai 60,000 a hannunsu.