✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farashin kayan abinci ya tashi a Taraba bayan dawo da amfani da tsofaffin kudi

Lamarin ya canza je bayan umarnin CBN na karbar tsofafin kudi

Farashin kayan amfanin gona da na dabbobi ya karu a kasuwannin Jihar Taraba sanadiyyar dawo da hada-hada da tsofaffin takardun kudi.

A ranar Litinin ce dai Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ba bankunan kasuwanci da ke kasar nan umarnin ci gaba da karbar tsofaffin takardun N1,000 da N500 da kuma N200, har nan da karshen watan Disamba.

Sai dai wakilinmu ya gano cewa a kasuwar Iware da ke ci a duk ranar Talata, an sami karin farashin kayan amfanin gona da na dabbobi a sanadiyyar amfani da tsofaffin kudin.

Binciken da wakilin namu ya gudanar ya gano cewa farashin masara da gyada da wake da shinkafa da na dabbobi ya karu.

Misali, a buhun masara wanda aka sayar a makon jiya a kan N14,000, a yau ya koma N18,000.

Farashin buhun shinkafa kuwa wanda aka sayar a kan N16,000, a yanzu ya karu zuwa tsakanin N18,000-N20,000.

Haka farashin Shanu da kananan dabbobi su ma sun karu.

Binciken ya nuna cewa saniyar da aka sayar N220,000 a makon jiya yanzu ta kari da kimanin N50,000.

’Yan kasuwar da wakilinmu ya zanta da su sun ce kafin a bayar da umarnin karban tsofaffin takardun kudin, ana ciniki ne ta hanyar tura kudi ta banki, wato ‘transfer’.

Wani dan kasuwa mai suna Abubakar Sani ya ce kayan da aka biya da sabbin takardun kudi sun fi sauki a kan wadanda aka saya ta hanyar transfer.

Sai dai ya ce bayan umarnin canza kudaden, lamarin ya canja a kasuwar ta lware ranar Talata.