Binciken jaridar Daily Trust ya gano cewa farashin kayan abinci ya fadi warwas a yankunan karkara na jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Sassan jihar da farashin kayan abinci ya karye sun kunshi Mutum Biyu, Garba-Chede, Maihula, Dakka, Garbabi, Tella Monkin da Jatau.
Ya zuwa lokacin da aka gudanar da binciken, ana sayar da masara sabuwar girbi a kan farashin N8000 a kasuwar Maihula yayin da farashinta ya ke N7000 a Dakka.
Haka kuma ana sayar da buhun masara sabuwar girbi a kan N12,000 a kasuwar Mutum Biyu da kuma N11,000 a kasuwar kauyan Garba-Chede.
Wakilanmu sun gano cewa, ana sayar da masara tsohuwar ajiya a tsakanin farashin N13,000 zuwa N15,000 a kasuwannin kauyukan da ke fadin jihar.
Karyewar farashin kayan hatsin na zuwa ne a yayin da manoma a fadin jihar ke ci gaba da girbi bayan samun yabanyar amfanin gona.
Farashin sabuwar shinkafa ‘yar gida ya sauko daga N17,000 inda a yanzu ake sayar da duk buhu guda a kan N12,000.
A yanzu dai ana sayar da duk kwano daya na shinkafa ‘yar gida a kan N900 sabanin yadda aka rika cinikayyarsa a kan N1,200 a makon da ya shude.
Sauran kayan abinci da su ma farashinsu ya fado sun hadar da doya, rogo, wake da kuma gyada.
Wani manomi, Alhaji Ali Maihula ya shaidawa wakilanmu cewa, rahusa ta farashin kayan abincin da ake samu a yanzu na da nasaba ne da yadda manoma suke samun karin yabanya da kuma albarka ta amfanin gona da suke girbewa a bana.
Ya ce a hakan ma farashin kayan abincin ya fi sauki a yankunan karkara da suke fuskantar kalubale wajen fito da amfanin gonakinsu sakamakon rashin hanya mai kyau.