A watanni bakwai da kungiyar Boko Haram ta kashe farar hula 223 da sojoji 82 da kuma ’yan sanda bakwai, kamar yadda kididdigar Aminiya ta tabbatar.
Binciken ya kama nuna farar hula 21 da sojoji 13 ne suka jigata a tsawon lokacin.
Wannan ta’asar ta faru ne a sassan jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa, daga watan Janairu zuwa 2 ga watan Agusta, 2020.
Makonni biyu da suka gabata, ’yan bindiga sun kai hari ga ayarin motocin Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, a hanyarsa ta zuwa Baga.
Tabarbarewar harkokin tsaro a yankin Arewa maso Gabas ya sa gwamnonin yankin ziyartar Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Litinin.
A taron da suka yi, sun jaddada masa cewar mayakan Boko Haram na kara samun mabiya, kuma akwai bukatar a mayar da ’yan gudun hijira garuruwansu don su ci gaba da noma gonakinsu.
— Soji da farar hula da aka rasa tsawon lokacin
A ranar 3 ga watan Janairu, an kashe farar hula uku a kauyen Bila-Ambokdar da ke Karamar Hukumar Chibok, sai kuma soji hudu da mutum 11 sun jigata a ranar 4 ga watan Janairu a garin Jakana na Jihar Borno.
Ranar 6 ga watan Janairu, an kashe ’yan sanda uku a kauyen Kundori da ke Karamar Hukumar Konduga, a yayin da wasu biyu suka samu raunuka a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, duk a Jihar Barno.
A Gamboru, Karamar Hukumar Gambarun Ngala ta Jihar Barno, an kashe farar hula 30, sai kuma mutum 35 da suka samu raunuka a ranar 7 ga watan Janairu.
Haka nan, a ranar 7 ga watan Janairu, soja takwas da farar hula takwas sun rasa rayukansu a Karamar Hukumar Monguno.
A ranar 10 ga watan Janairu, ’yan ta’adda sun kashe farar hula uku a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a Karamar Hukumar Konduga ta Jihar Borno.
A ranar 17 ga watan Janairu, sojoji biyar suka rasa rayukansu da wasu mayakan Boko Haram hudu a sansani soji na Firgi da ke Karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno.
A ranar 18 ga watan Janairu, sojoji hudu sun rasu a kan titin Bama zuwa Gwoza a Karamar Hukumar Gamboru-Ngala. Sai kuma sojoji 8 da suka rasu a ranar 21 ga watan Janairu a garin Mainok.
An kashe farar hula 23 a kauyen Lura na Karamar Hukumar Dikwa a ranar 23 ga watan Janairu; sai wasu hudu suka rasa rayukansu washegari a kauyen Muna Galti da ke Karamar Hukumar Jere.
Haka kuma a ranar 29 ga Janairu, farar hula uku sun mutu, biyu sun jikata a hanyar Damaturu-Maiduguri a Karamar Hukumar Konduga ta Jihar Borno. Sai kuma soji biyu da aka kashe a ranar 21 ga watan Fabrairu a Karamar Hukumar Gombi ta Jihar Adamawa.
A Masallacin Bulabulin da ke Gwoza, farar hula uku sun musu yayin da 13 suka jigata a ranar 25 ga watan Janairu.
Farar hula uku sun rasa rayuwarsu a kan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, biyu suka jigata, sai kuma sojoji biyu da aka kashe a ranar 21 ga watan Fabrairu.
An kashe Sojoji uku, hudu kuma sun jigata a ranar 4 ga watan Maris a Damboa. ’Yan sanda bakwai da farar hula daya sun rasu a garin Dapchi a ranar 5 ga watan Maris.
A ranar 21 ga watan Maris, sojoji 47 sun rasa rayukansu a kauyen Gorgi da ke Borno yayin da farar hula uku suka rasa ransu.
Haka nan kuma farar hula bakwai sun rasa rayukansu a ranar 13 ga watan Fabrairu kan titin Auno-Maiduguri-Damaturu, sai kuma mutum daya da aka kashe a ranar 18 ga watan Afrailu a Buni Gari.
Farar hula 35 sun rasu a Usmanati Goni a ranar 13 ga watan Yuni a Nganzai a Borno, yayin da farar hula 16 da sojoji tara suka rasu a babbar hanyar Damboa zuwa Maiduguri.
Farar hula biyar sun mutu a Moduri, Kalewa da Ngurori a ranar 21 ga watan Yuni a Magumeri da ke Borno.
Farar hula biyu sun mutu a Damasak a ranar 4 ga watan Yuli.
— Boko Haram na kara samun mabiya
Gwamnonin Arewa maso Gabas sun sanar da shugaban kasa a zaman da suka yi da shi ranar Litinin cewar mayakan Boko Haram na cigaba da samun magoya baya, tare da rokon a mayar da ’yan gudun hijira kauyukansu don cigaba da noma gonakinsu.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa ta Gabas, kuma gwamnan jihar Barno, Babagana Zulum, ya bayyana haka bayan fitowa daga ganawarsu da Shugaba Buhari da shugabannin tsaro, a Fadar Shugaban Kasa.
Zulum ya ce sun roki shugaban kasa a sama wa mutanensu tsaro da damar da za su ci gaba da gudanar harkokin rayuwa. A kuma bai wa ’yan sanda kayan aikin zamani da za su taimaka wajen rage ta’adanci a kasa.
Ya kuma ce taron ya taba abubuwa da suka shafi matsalolin yankinsu kamar na tsaro da tabarbarewar abubuwan more rayuwa da maganar hakar danyen man fetur da raya kogin yankin.
Zulum ya kuma ce sun roki Gwamnatin Tarayya ta magance abubuwan ke haddasa ta’addanci a yankin.
— Dole shugabannin tsaro su kara kaimi, inji Buhari
Buhari ya kara nanata wa shugabannin tsaro cewar dole ne su kara kaimi domin karar da matsalolin tsaro a Najeriya.
Bayan ya saurari abun da gwamnonin Arewa maso Gabas din suka je masa da shi, ya bukace su da su jinjina wa sadaukar da kai da sojojin Najeriya ke yi.
— Alkawarin samar da tsaro
Ya ce annobar COVID-19 ta kawo matsalar kudi, amma duk da haka gwamnatin za ta ci gaba da yin bakin kokarinta na ganin an magance al’amarin.
Buhari ya kuma ce mulkin Jam’iyyar APC zai kawo tsaro a kasa saboda shi ne kashin bayan ci gaban kowace gwamnati kuma yana daga cikin muhimman abubuwan da suka gabatar domin a zabe su.
Sakataren Gwamnati, Boss Mustapha da Shugaban Ma’aikatan Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari da Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Babagana Monguno da kuma hafsoshin tsaro, duk sun ba da tabbacin za a samar tsaro.
Sun kuma tabbatar da karin fahimta tsakinin jami’an tsaro da gwamnatocin jihar da sarakuna da al’ummomi kasa.
— An kori ’yan ta’adda daga Arewa mas Gabas —Buratai
Babban Hafsan Soji, Tukur Buratai, ya bayar da bayanin yanayin tsaro a kan Boko Haram, inda ya ce an kore su daga jihohin yankin Arewa maso Gabas. Ya ce, Jihar Borno kadai ta rage.
“Muna hada kai da al’umma da sarakuna da kuma kara kaimi. Abun da muke bukatar shi ne, a kara hakuri. Ba za mu gaza ba”, inji shi.