A farkon shekarar da muke ciki, wata tawaga ta masu kade-kade da raye-raye daga kasar Lebanon suka yi wasan kwaikwaiyo na farko a Saudiyya inda suka ba da labarin wani sadauki da ya yi suna kafin isowar addinin Islama da kuma masoyiyarsa ‘yar kabilar Bedouin mai suna Abla.
Wannan yana cikin shirye-shirye masu nishandantarwa da aka bullo da su a cikin kasar mai ra’ayin rikau.
Yana cikin gagarumin shirin Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman da ake yi wa lakabi da bision 2030, na mayar da kasar daga wadda take dogaro da man fetur zuwa ta mai kazar-kazar ta fuskar tattalin arziki.
Yayin wata ziyara da ya kai Birtaniya da Amurka da kuma Faransa, Yarima Mohammed mai shekara 32 , ya rika neman taimakon kasashen waje a kan yadda zai cimma wannan buri nasa.
A ranar Litinin ne kungiyar kade-kade da raye-raye na Paris ta sa hannu da Saudiyya a kan yadda za ta taimaka wa kasar kafa tata kungiyar kade-kade da raye-raye ta kasar Saudiya kamar yadda BBC ta ruwaito.
An soma shirye-shiryen bude gidan kade-kade da raye-raye na farko a birnin Jeddah wanda shi ne birni mafi girma na biyu a kasar
Ministan raya al’adun gargajiya na Saudiyya ya yi shelar wani sabon tsari bayan tattaunawar da suka yi da takwaran aikinsa na Faransa:
Gajerun fina-finan Saudiyya za su shiga cikin bikin baje kolin fina-finan Cannes a karon farko da za a yi a shekarar da muke ciki.
Hakan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen bude gidan sinima na farko a Riyadh a watan da muke ciki, ga kuma bangaren harkar fina-finai na cikin gida da ke samun karbuwa.
Sai dai yarjejeniyar raya al’adun gargajiya mafi girma da kasashen biyu suka sa hannu a kai, za ta bai wa Faransa damar kawo sauyi a akasarin wuraren da babu kowa, zuwa gidan ajiye kayan tarihi.
Manufar shirin ita ce a samar da wurin adana kayan kofai na kasar, ciki har da zane-zanen layin dogo na Hejaz da ya tashi daga Damascus zuwa Medina, wanda TE Lawrence ya kai wa hari lokacin da Larabawa suka yi bore.
A watan Fabrairu ne Saudiyya ta ce za ta zuba jarin fam bilyan 64 a bangaren nishadi a cikin shekara goma masu zuwa.
Wannan dai wani sauyi ne ake gani a cikin kasar da wasu ke yi wa kallon mai tsaurin ra’ayi, inda askarawan kasar kan hana duk wasu kade- kade da raye -raye da ake yi a bainar jama’a.