Wani sabon rikici ya dabaibaye Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma (NWDC) kan shirin daukar nauyin dalibai zuwa karatu a kasashen waje.
Wannan dambarwar ta kunno kai ne bayan sanarwar da hukumar ta fitar na shirin daukar nauyin daliba domin karatun jami’a daga yankin.
Majalisar Amintattun Hukumar ta ce ba a taba tattaunawa kan shirin a zamanta ba, a yayin da majalisar gudanarwar Huukumar ke ikirarin cewa ta sanar da su ta wata wasika da ta aike musu.
Wasu mambobin Kwamitin Amintattun hukumar da wakilinmu ya zanta da su sun zargi hukumar gudanarwar da yin gaban kanta.
- Hajj 2025: Maniyyatan Kaduna za su fara tashi ranar 14 ga watan Mayu
- Wata mata ta auri maza biyu a lokaci guda a Kano
A daya gefen kuma Manajan Daraktan Hukumar, Farfesa Shehu Abdullahi Ma’aji ke cewa ya sanar da Shugaban Kwamitin Amintattun, Lawal Samaila Abdullahi, game da shirin daukar nauyin dalibai kamar yadda dokar da ta kama hukumar ta tanadar.
Daukar nauyin dalibai: Jagororin NWDC na nuna wa juna yatsa
A makon jiya ne rikicin ya kazance bayan hukumar ta fitar da sanawar gurabun daukar nauyin daliban yankin domin karatu a fannonin koyara da kuma kimiyyar sadarwar zamani (ICT) a kasashen waje.
Za a dauki nauyin daliban yankin ne domin fara karatu a shekarar karatu ta 2025/2026 a jami’o’in kasashen Indiya da Malaysia da Kanada da Indonesia da kuma China.
Sanarwar hukumar ta ci karo da matsayar Gwamnatin Tarayya wadda Ministan Ilimi, Tunji Alausa ya sanar cewa gwamnati ta dakatar da duk shirye-shiryen daukar nauyin dalibai zuwa kasashen waje na tsawon shekaru biyar.
Kwanaki kalilan bayan sanarwar da hukumar ta fitar ne wasu daga cikin mambobin Kwamitin Amintattun hukumar suka bayyana cewa ba a taba tattaunawa game da shirin daukar nauyin karatun daliban ba a zamansu.
Daya daga cikinsu ya shaida wa wakilinmu cewa bai taba sanin akwai shirin daukar nauyin daliban ba, kuma ba a taba magana a kai ba a duk zaman da suka yi. Ya yi zargin “wasu daga waje na da hannu wajen kitsa sanarwar ba tare da bin tsarin da doka ta tanada ba.”
Wakilinmu ya tuntubi wasu mambobin kwamitin amintattun, amma suka ke cewa uffan, inda suka bukaci ya nemi Shugaban Kwamitin Amintattun.
Sanarwar bogi ce — Kwamitin Amintattu
Shugaban Kwamitin Amintattun Hukumar Kula da Ci-Gaban Yankin Arewa Maso Yamma, Lawal Samaila Abdullahi, ya bayyana sanarwar shirin daukar nauyin daliban zuwa kasar waje a matsayin na bogi.
Ya ce, “Sanarwar bogi ce. Na san sauran mambobin kwamitin amintattu na korafi a kan sanarwar, amma ba zan iya cewa ga ainihin abin da ya faru ba, saboda ba mu taba tattaunawa a kai ba. Amma dai za mu yi zama a ranar Alhamis din nan domin tattaunawa game da abi.”
Da muka tambaye shi ko majalisar gudanarwar hukumar ce ta fitar da sanarwar ita kadai, sai ya amsa da cewa a halin yanzu babu majalisar gudanarwar hukumar saboda ba a nada su ba a hukumance.
Lawal Samaila Abdullahi ya ki amsa tambayarmu game da wasikar da manajan daraktan hukumar ya yi ikirarin aike wa kwamitinin amintattun. Amma ya bukaci wakilin namu ya jira sakamakon zaman da za su yi ranar Alhamis.
Ba mu saba doka ba —Majanan Darakta
Amma a martaninsa, Manajan Daraktan Hukumar, Farfesa Shehu Abdullahi Ma’aji, ya bayyana karara cewa aikinsu shi ne sunar da Shugaban Kwamitin Amintattu game da duk wani babban tsari mai muhimmanci, kuma sun sun riga sun yi hakan, ta wata takarda da suka aike masa a ranar 28 ga watan Afrilu, wanda wakilinmu ya samu ganin kwafinta.
Sanarwar ta ce, “ina farin cikin sanar da kai game da shirin da muke son yi na daukar nauyin dalibai daga jihohi bakwai da ke wannan yanki. Manufar shirin shi ne ba su damar samun ilimi mai zurfi a manyan jami’o’in kasashen waje…
“Wannan zai ba wa matasan yankin damar samun ilimi da da kwarewa daidai da takwarorinsu a ko’ina a duniya domin bayar da gudummanwar ci-gaban wannan yanki.
“Nan gaba za mu fitar da cikakken bayani game da tsarin da za a bi da sharuddan cancanta. Don haka muke sanar da ku domin ku shaida,” in ji sanarwar.
Farfesa Ma’aji ya ce “iya abin da muka yi shi ne neman fara tantance dalibai, babu wanda muka tura kasar waje. Hasali ma tsare-tsaren muke kokarin farawa, babu dokar ko umarnin da muka saba tunda har yanzu babu wanda muka fara magana da shi.
“Muhimmin abin shi ne muna yin wannan shirin ne domin amfanin ’ya’yanmu da marasa galihu, su kuma abin da ba sa so ke nan. Wannan shi ne gaskiyar abin da ke faruwa.
“Sa’annan ba kudaden dungurungum za mu sa domin daukar nauyin shirin mu kadai ba, hadin gwiwa ne kasa da kasa, inda gwamantocin kasashen za su biya duka ko rabi, mu kuma mu biya ragowar.
‘Minista ya san da maganar’
“Kar ka manta cewa an bar yankinmu a baya a fannin ilimi, shi ya sa muka ga ya dace mu gabatar da wannan shiri a matsayin wani mataki da zai magance wannan matsala,” in ji shi, yana mai zargin kwamitin amintattun da “neman kirkiro kananan maganganu a kan abin da babu shi.”
Ya bayyana cewa, “Ni da kaina na je na sami ministan ilimi ya bayyana masa abin da shirin ya kunsa kuma ya fahimta. Mu abin da muke nema shi ne duk abin da zai amfani yankinmu ya kawo masa ci-gaba. Kuma na gaya musu karara cewa babu gudu, babu ja da baya a kan wannan.”
Farfesa Ma’aji ya yi watsi da zargin da ake na katsalandan din wasu daga wajen hukumar, da cewa, “idan ma zargin ya tabbaba, ai ba laifi ba ne idan aka shiryatar da mutum ga yin abin da ya dace.”
Game da hukumar NWDC
A watan Yulin 2024 aka kafa Hukumar Raya Arewa maso Yama (NWDC) kuma an tsara ta ne kamar takwarorinta NDDC da kuma NEDC masu alhakin raya yankunan Neja Delta da kuma Arewa maso Gabas.
Shugaba Bola Tinubu ya kama hukumar ce domin magance matsalolin ci-gaba da bunkasa tattalinarzikin yankin Arewa maso Gabaas, wanda ya kunshi jihohin Jigawa da Kaduna da Kano da Katsaina da Kebbi da Sakkwato da kuma Zamfara.
Bayan wata biyu da kafa hukumar aka nada kwamitin amintattu karkarshin jagorancin Lawal Samia’ila Adullahi, da kuma Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji a matsayin Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa.
Ayyukan hukumar NWDC, wadda hedikwatarta za ta kasance a Kano, sun kunshi samar da gagarumin ci-gaba da bunkasa tattalin arziki da yanayin zamantakewa a yankin mai yawan al’umma sama da miliyan 45.
Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayar da filin mai darajar naira biliyan biyar inda za a gidan hedikwatar hukumar, a yayin da Farfesa Adamu Abubakar Gwarxo ya ba da gudummawar gini mai hawa bakwai a matsayin hedikwatar hukumar na wucin gadi har zuwa lokacin da za a kammala ginin hedikwatar ta dindindin.
An kafa hukumar ne a daidai lokacin da Arewa maso Yamma ke fama da matsaloli masu yawa, kamar rashin tsaro, yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, da kuma karancin ababen more rayuwa.
Rikicin da ya gabata
Idan ba a manta ba rikicin da ya fara dabaibaye hukumar shi ne wanda ya kunno kai makonnin kadan baya an kafa ta, kan wanda zai kasance shugabanta.
Dokar hukumar NWDC ta tanadi cewa shugabancin hukumar zai kasance na karba-karba a tsakanin jihohi bakwai na yankin, a bisa jerin abajadiyya.
Bisa haka, ya kamata Jihar Jigawa ta fara jagorantar hukumar, amma wasu suka kekashe kasa cewa dole shugabanta na farko ya fito da Kano.
Wannan dambarwa ta da dole aka sake mayar da dokar gaban Majalisar Dokoki ta Kasa, ta yi masa kwaskwarima.
Dokar da ta kafa hukumar
Dokar da ta kama Hukumar Kula da Ci- Gaban Arewa maso Yamma (2024) ta bayyana cewa Manajan Darakta da Shugaban Kwamitin Amintattu kowanne aikinsa da baban ne, amma suna taimaka wa juna domin kawo ci-gaban yankin.
Dokar ta bayyana cewa Manajan Daraktan shi ne babban jami’in gudanarwan hukumar kuma shi ke da alhakin kula da ayyukanta na yau da kullum, ciki har da aiwatar da tsare-tsare da shirye-shirye da suka samu sahalewar kwamitin amintattu.
Shi ke da alhakin gudanar da ayyukan ababen more rayuwa da tattalin arziki da ci-gaba ta hanyar hadin gwiwa da hukumomin gwamnatin da suka dace, da masu zuba jari da al’ummomin a abin ya shafa; hakazalika, shi ke da alhakin bayar da bayanai kan halin da ake ciki da kuma kalubalen da hukumar ke fuskanta.
A daya bangaren kuma, Shugaban Kwamitin Amintattu ke jagorantar kwamitin daraktoci wadda ke sanya alkibla ga hukumar tare da sanya ido a kan ayyukanta. Su ke da alhakin tsara manufofi da kuma hadafi na tsawon lokaci ga hukumar.
Shi ke da alhakin tabbatar da yin komai a fili cikin gaskiya a duk al’amuran hukumar da nade-nadenta, suna masu ba da shawara ga manajan darakta da hukumar gudanawar hukumar, tare da wakiltar hukumar a manyan taruka.
Kwamitin amintattun, shugaba da mamnabobi 14 da suka hada da wakilai daga kowacce daga jihohi bakwai da ke yankin da kuma mutum daya da ke wakiltan kowanne daga cikin shiyyoyin siyasa shida da ke kasar nan.
Ba a jima da kafa hukumar ba, wadda watan da ya gabata ne ma ta samu wurin da za ta yi amfani da shi a matsayin hedikwatanta na wucin gadi.
Idan aka aiwatar da shirin daukar nauyin daliban cikin nasara, zai zama babban aikin farko da hukumar ta gudanar.