Akalla mutum shida ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani sabon hari Karamar Hukumar Barikin Ladi da ke Jihar Filato.
’Yan bindigar sun kuma jikkata mutane da dama a hare-haren da suka kai unguwannin Marit da Gashish a ranar Litini.
Aminiya ta samu labarin cewa an garzaya da wadanda suka ji raunin asibiti, bayan harin da aka kai a yayin da mutane suke tsaka da barci a cikin dare.
Shugaban Karamar Hukumar Barikin Ladi, Hon. Stephen Pwajok Gyang, ya bayyana cewa an riga an yi jana’izar mamatan yana mai yin Allah wadai da harin.
- Hajj 2025: Maniyyatan Kaduna za su fara tashi ranar 14 ga watan Mayu
- Wata mata ta auri maza biyu a lokaci guda a Kano
- NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ‘Yan Gwagwarmaya Ke Shiga Tasku A Najeriya?
A yayin ziyarar dubiya da ya kai Babban Asibitin Barikin Ladi, Hon. Pwajok ya nuna takaici bisa yadda bata-gari ke mayar da hannun agogo, duk da kokarin da hukumomi ke yi na tabbatar da zaman lafiya a karamar hukumar.
Ya yi wa majinyata addu’ar samun sauki da kuma rahama ga mamata, tare da jinjina wa kokarin ’yan banga da sauran jam’an tsaro a yankin.
Wannan hari na zuwa ne makonni kadan bayan makamancinsa a yankin Bassa da Bokkos inda aka kashe sama da mutum dari ciki har da mata da kananan yara.
Hare-haren dai sun biyo bayan rahoton harbe-harbe da kuma kashe dabbobi ta hanyar guba a yankunan kananan hukumomin Bassa da Riyom da kuma Mangu.