✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Faransa ta daure dan wasan Algeria kan goyon bayan Gaza

Zuwa yanzu Isra’ila ta kashe Falasdinawan da yawansu ya haura dubu 22 a Gaza.

Wata Kotu a Faransa ta yi wa dan wasan gaba na Algeria da ke taka leda a Nice, Youcef Atal daurin talala har na tsawon watanni 8.

Kotun ta ce ta yanke wannan hukuncin ne bayan tuhumarsa da wallafa wani bidiyo a shafinsa na sada zumunta da ke da alaka da addini dangane da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa al’ummar yankin Gaza.

Kotun ta bayyana cewa, bidiyon na Atal zai haddasa tsana ta hanyar amfani da addini wanda kuma kai tsaye ke goyon bayan ta’addanci bayan da bidiyon ke addu’ar neman nasara ga al’ummar Gaza.

RFI ya ruwaito cewa kotun hukunta manyan laifuka ta birnin Nice ta kuma ci tarar Atal yuro dubu 45 dangane da bidiyon yayin da a bangare guda kungiyarsa ta dakatar da shi.

Matashin dan wasan mai shekaru 27 wanda ke sahun ‘yan wasan da za su wakilci Algeria a gasar cin kofin Afrika da ke tafe cikin watan nan, tuni ya nemi yafiya kan bidiyon da ya wallafa wanda ya ce tun a lokacin ya goge shi.

Sakon bidiyon na Atal dai na dauke da malamin addini Mahmoud al-Hasanat wanda ke bayani kan kisan kare dangin da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa tare da addu’ar Allah ya basu nasara kan Isra’ila.

A cewar kotun, bidiyon na Atal ba ya kunshe da kalaman neman zaman lafiya face kalaman nuna kyama ga Yahudawa wanda ke matsayin babban zunubi.

Bayanai sun ce dan wasan yana da damar daukaka kara nan da kwanaki goma da ayyana hukuncin da kotun ta yi.

Zuwa yanzu Isra’ila ta kashe Falasdinawan da yawansu ya haura dubu 22 daga ranar 7 ga watan Oktoba.