Dan kasuwa Mahadi Shehu da ya yi bidiyon fallasa da zargin zambar kudade a Gwamnatin Jihar Katsina ya gurfana a gaban kotu.
An ga Mahadi Shehu yana tafiya da kyar yana dogara sandar guragu a lokacin zaman Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta ta Katsina.
- Kungiyar OPC ta kone kauyen Fulani ta kashe mace mai ciki a Oyo
- An rufe makarantu a Kwara kan rikicin sanya Hijabi
- Ranar Mata ta Duniya: Aisha Buhari ta bukaci kariya ga ’ya’ya mata
Gwamnatin Jihar Katsina ta yi karar dan kasuwar mazaunin Kaduna ne bis zarginsa da zambar intanet bayan jami’an tsaro sun tsare shi a Abuja.
Kwamishinan Shari’an Jihar, Ahmad El-Marzuq, ya yi karar Mahadi ne a watan Fabrairu, yana tuhumar sa da yada karairayi a kan Gwamnatin Jihar a shafukan sa da zumunta.
A cewarsa, takardun bayanan da dan kasuwar ya yi ta yadawa yake kuma dogaro da su wajen zargin almundahan, duk na jabu ne.