Fassarar Salihu Makera
Huduba ta farko
Hamdala da taslimi
Bayan haka, ga shi dai kwanakin Ramadan suna ta gudu, mun daf da shiga goman karshe wanda shi ne dama ta karshe ga wanda ya yi sakaci a farkon watan, ko kuma ya zama cikaton alheri ga wanda ya kyautata ya bayar da abin da ake so a baya.
Ya ku masoya! Goman karshe na watan Ramadan kasuwa ce babba da masu tsere suke tsere a cikinta. Lokaci ne da wanda ya yi sakaci ke matsuwa a cikinsa, ake jarraba masu himma a cikinsa, ake tantance ma’abuta Lahira da ma’abuta duniya.
Da yawa masu huduba sun yi magana, masu wa’azi sun yi wa’azi, masu nasiha sun yawaita nasiha kan falalolin wadannan kwanaki da darare, zukatan da suka jiku da imani sun amshi wannan kira, wata jama’a ta amshi kiran ta bi hanyar muminai, ta koma cikin masu ruku’u da sujada, hawayensu na kwarara a tsakiyar dare mai duhu, kuma Ubangijinka Yana ji kuma Yana amsa musu, Ubangijinka bai zama Mai zaluntar bayi ba.
Amma wata jama’a ta ji kiran amma kamar ba ta damu ba. Suna jin muminai suna salloli da tsayuwar dare don ibada ga Ubangijinsu, amma su kamar ba su da bukata, kai kamar an yi musu lamunin Aljanna, shin masu wannan watsewa ba za su yi tunani ba? Shin masu wannan sakaci ba za su sake tunani ba ne?
Ya ku Musulmi! Ranakun watanku suna raguwa, dararensa masu daraja suna karewa suna masu shaida a kan abin da kuka aikata, suna kiyaye abin da kuka yi, su masu taskace kyawawan ayyukanku, masu tsarewa da adana su har an kira ku a Ranar Kiyama: “A ranar da kowane rai ke samun (sakamakon) abin da ya yi.” Ubangijinku Yana kira: “Ya ku bayiNa! Abin sani ayyukanku ne Nake kidaya muku kuma zan saka muku a kai. Duk wanda ya samu alheri sai ya gode wa Allah, wanda ya samu wanin wannan kuma, kada ya zargi kowa sai kansa.”
Wannan watanku ne kuma wannan ne dama ta karshe, mutum nawa ne ya fara azumin bai kawo yanzu ba, ko ba zai kammala shi ba? Kuma mutum nawa ke kwadayin dawowarsa a bana amma bai riske shi ba? Shin ba za ku yi nazari kan ajali da makomarku ba? Shin ba za ku dubi yaudarar da dogon buri ke yi muku ba?
Ya ku Musulmi! Idan akwai mai gargadi ga rayuka ko mai wa’azi ga zukata, to, bai wuce dan abin da ya saura na kwanakin Ramadan ba. Saura kwana nawa ne? Muna daf da shiga goma na karshe, sauran kwanakin da Annabinku (SAW) yake matukar zage damtse domin bauta wa Allah. A ashirin na farko yana hada sauran ibadoji da Sallah da barci, amma da goman karshe ya shigo, sai ya tattara shimfidarsa ya ja mazagin wadonsa ya kaurace wa shimfidar barcinsa, ya tashi iyalansa ya kwankwasa kofar Fatima da Aliyu (Allah Ya yarda da su) yana mai cewa: “Ashe ba za ku tashi ku yi Sallah ba?” Sannan ya fuskanci dakunan matansa yana umarni tare da bayyana cewa: “Ku farka Ma’abuta Babban Gida (Ahlul Bait), da yawa masu sutura a duniya tsirara suke a Lahira.” Annabi (SAW) ya kasance idan goman karshe na Ramadan ya zo, ba ya barin duk wanda zai iya tsayuwar dare daga cikin iyalinsa a kwance face ya tashe shi.
Kuma magabatan kwarai sun fi sauran mutane bibiya da koyi da Annabi (SAW). Ya zo a cikin Muwadda na Imam Malik (Allah Ya lullube shi da rahamarSa) cewa Umar dan Khaddabi (RA) ya kasance yana Sallah gwargwadon yadda Allah Ya so, har sai dare ya raba, sai ya tashi iyalansa yana ce musu “Sallah! Sallah!” Sannan sai ya karanto wannan aya: “Ka umarci iyalinka da yin Sallah da hakuri a kanta. Ba Mu tambayarka dukiya, Mu ne masu azurta ka, kuma kyakkyawar karshe ta masu takawa ce.”
Sufyanu Suri (Rahimahullah) ya ce, “An so idan goma karshe ya shigo (Musulmi) ya yi kokari da daddare ya yi kokari a cikinsa, ya tashi iyalinsa da ’ya’yansa su yi Sallah matukar za su iya hakan.”
Wata mata daga cikin magabatan kwarai ta fada wa mijinta cewa: “Hakika dare ya tafi alhali akwai doguwar tafiya a gabanmu, sannan guzirinmu kadan ne, kuma ayarin salihai ya yi mana nisa, mu ne muka saura a hanya!”
Ya ku Musulmi! Ku san darajar zamaninku, ku girmama mafi falalar lokacinku, ku gabatar da aikin alheri domin kanku. Kada ku bata lokacinku a cikin abin da ba neman kusanci ba ne ga Allah. Ba da buri ake kyautata zaton alheri ba, ana kyautata zato ne da kyautata aiki. Sanya ran samun rahama tare da aikata sabo wani nau’i ne na wauta da tabewa. Ba da kuka da share hawaye ake tsoron Allah ba, ana tsoron Allah ne ta barin abin da ake tsoron ukuba a kansa.
Ya ku masoya! Ku gabatar da aikin alheri ga kanku, ku tsayu kuma ku yi kankan da kai. Uwar Muminai A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ce: “Ya Manzon Allah! Shin idan na riski daren Lailatu Kadri me zan ce a cikinsa? Sai ya ce: “Ki ce: “Allahumma innaka afuwun tuhibbul afuwa, fa’afu anni.” Ma’ana “Ya Ubangiji! Kai Mai yawan afuwa ne, Kana son afuwa, Ka yi min afuwa.” Ku yawaita wannan addu’a a cikin goman karshe. Ubangijinku Ya ce, “Idan bayiNa suka tambaye ka game da Ni, to, lallai ne Ni ina kusa, Ina amsa kiran wanda ya yi kira idan ya kira Ni. Don haka su amsa Min, kuma su yi imani da Ni, damaninsu suna shiryuwa.”
Ko kun san su wane ne wadannan bayi? Halittu dukkansu bayin Allah ne, sai dai kuma wadannan bayi kebantattu ne. Su ne bayi daga ma’abuta addu’a, bayin da suke jiran a amsa musu, su ne masu addu’a cikin kankan da kai, masu addu’a tare da babbar fata, masu kankan da kai wajen kwadayin amsawa; “Idan bayiNa suka tambaye ka game da Ni, to, lallai Ni ina kusa…”
Lallai addu’a tana da wani sha’ani mai ban mamaki da tasiri babba wajen kyan karshe da gyara hali da dukiya da dacewa a cikin ayyuka da albarka a cikin arziki. Shin ba ku ganin wanda ya dace da rabo ta wajen addu’a, yana samun rabonsa daga kankan da kai da fakewa ne a wurin Allah a kowane hali ba? Shi ne yake komawa ga Allah a dukkan bukatunsa ya yi addu’a, a yi masa addu’a, ya rabauta da addu’arsa ta kashin kansa da ta waninsa. Mahaifansa suna son sa, ’ya’yansa suna yi masa da’a, mutanen da suke kusa da shi dukansu suna kewaye shi da addu’a. Mahaliccinsa Yana son sa don haka ya fawwala karba masa. Sai halayensa su kyautata, aikinsa ya yi kyau, sai hannuwa su dagu sama, harsuna sun daukaka wajen yi masa addu’a. Allah Yana lura da shi da datar da shi, sha’aninsa yana kyautata tare da dacewa.
Yaya za a kwatanta shi da wanda aka haramta masa haka, wulakatacce wanda bai dandani zakin ganawa da Ubangijinsa a Ramadan ba? Yaya za a hada shi da wanda ya ji kunyar bauta wa Ubangijinsa, ya yi girman kai daga rokon Ubangijinsa? Abin haramtawa da ya rufe kofar rahama ga kansa, ya lulluba da tufar gafala?