Bayan kimanin mako biyu da Hukumar Tsaron kasa (SSS) ta wanke tsohon Gwamnan Jihar Borno Ali Modu Sherrif kan alaka da kungiyar Boko Haram, jaridar Premium Times da ke fitowa a intanet ta ce ta samu wani faifan bidiyo da ke nuna Shugaba Goodluck Jonathan yana nuna shi da kansa ya gamsu cewa akwai doguwar alaka a tsakanin tsohon Gwamnan da wanda ya kafa kungiyar.
Faifai bidiyon wanda aka dauka a Afrilun 2013 a lokacin da Shugaba Jonathan ya ziyarci Borno, an ji shi yana bayyana Modu Sheriff wanda a wancan lokacin yake cikin jam’iyyar adawa ta APC da “abokin” Mohammed Yusuf, mutumin da ya kafa tare da jagorantar Boko Haram na wasu shekaru.
Yusuf ya mutu ne a lokacin da yake tsare a hannu n ’yan sanda, bayan a kama shi tare da wasu magoya bayansa sakamakon fafatawa tsakanin ’ya’yan kungiyar da jami’an tsaro.
shi
A lokacin ziyarar a watan Afrilun 2013 domin neman dattawa da mutanen Borno su amince da dimbin sojojin da aka tura jihar domin kawo karshen hare-hare, Shugaba Jonathan ya ce Boko Haram sun kankama ne suka yi karfi tare da daukar makami don yakar Najeriya a lokacin Gwamna Sheriff na mulkin jihar.
A matsayinsa na Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Shugaba Jonathan yana samun rahotannin tsaro a kai-a kai, kuma jama’a da dama suna da yakinin yana magana ne bisa ilimin da yake da shi a lokacin.
Bidiyon ya nuna Shugaban kasar sanye da babbar riga da hula rike da lasifika biyu a hannunsa a lokacin da yake jawabi ga masu saurarensa, inda yake kokarin kare mayar da Jihar Borno da sauran jihohin da ke Arewa maso Gabas a karkashin ikon sojoji.
Jonathan ya ce tura dubban sojoji zuwa yankin ya fara ne bayan tashin hankalin da ya biyo bayan kashe mu’assasin Boko Haram. Kuma Shugaban ya dauki lokaci yana kokarin tunawa da sunan jagoran Boko Haram din da aka kashe, inda a karshe ya bukaci masu saurare su tuno masa da sunan.
“Ehn ehn, mene ne sunan ehn ehn abokin Gwamna Sheriff?” Shugaban ya yi tambaya. Sai masu sauraren suka yi masa tafi suna dariya, wasu kuma suka amsa da Yusuf!
“Lokacin da aka kashe Yusuf, wannan ne masomin rikicin…” Shugaban ya ci gaba da fadi.
Muhammad Yusuf ne ya kafa Boko Haram, kuma kashe shi ba tare da gabatar da shi a gaban shari’a ba ne ya jawo kai miyagun hare-haren da ke barazana ga daukacin yankin Arewa maso Gabas.
A cikin faifan bidiyon, Jonathan ya ce dole ce ta sa aka tura sojoji a Jihar Borno ba don ana so ba, inda ya ce babu sojoji a Jihar Borno a shekarar 2001 da 2002 da 2003 har zuwa 2009. A lokacin ne aka kashe wannan mutum, kuma wannan ne mafarin tashe-tashen hankulan.
Akwai zarge-zarge kan alakar Ali Modu Sheriff da Boko Haram a zamanin da yake Gwamnan Jihar Borno tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011, inda majiyoyin hukumomin tsaro da na ’yan siyasa a jiharsa da kuma mazauna jihar suka yi da’awar Sheriff yana da kusanci na kut da kut da kungiyar da shugabanninta, har ma ya taba nada dan kungiyar a matsayin kwamishina.
A baya-bayan nan wani mai shga tsakani dan kasar Autireliya da ke aiki da gwamnatin Najeriya mai suna Stephen Dabis ya yi da’awar cewa wasu daga cikin manyan ’yan kungiyar sun shaida masa cewa Sheriff wani babban mai tallafa wa ayyukansu ne. Kuma a ranar 16 ga Disamban 2014 ne Hukumar SSS ta wanke Sheriff bayan ta gabatar da wasu mutum shida ciki har da tsohon mai tallafa wa Gwamna Kashim Shettima, inda ta ce wadanda ta gabatar din sun yi da’awar kirkirar karya ga dan Austireliyan da ya dogara da ita wajen da’awarsa.
Jaridar Premium Times ta ce wani bayanin sirri da ta ci karo da shi ya nuna Sheriff yana da alaka da kungiyar.
Takardar ta ce, Sheriff da kansa yake lura da yadda ake horarwa da tura mayakan kungiyar fagen fama daga Abeche da ke kasar Chadi. Kuma a yayin zaman Sherrif a Abeche yana sauka ne a masaukin Shugaban Chadi Idris Deby kamar yadda takardar tsaron ta bayyana.
Bayan da Sheriff ya koma Jam’iyyar PDP a watan Yulin 2014 ne sai ya zama babban abokin Shugab Jonathan, kuma daya daga cikin manyan shugabannin jam’iyya mai mulki, inda yake samun kariyar da ko gwamnoni ba su samu.
Sheriff dai ya sa musanta zargin cewa yana da alaka da kungiyar Boko Haram, sai dai wannansabon faifan bidiyo yana iya haifar masa da sabon kalubale a kokarinsa na wanke kansa game da alaka da hatsabibiyar kungiyar wadda a yanzu take zama babbar barazana.
Faifan bidiyo ya nuna Jonathan yana alakanta Modu Sheriff da Boko Haram
Bayan kimanin mako biyu da Hukumar Tsaron kasa (SSS) ta wanke tsohon Gwamnan Jihar Borno Ali Modu Sherrif kan alaka da kungiyar Boko Haram, jaridar…
