Fadar Shugaban Kasar Nijar ta ce Shugaba Mohammed Bazoum na nan kalau bayan yunkurin juyin mulkin da masu tsaron fadar suka yi, wanda ta ce bai yi nasara ba.
A cikin wata sanarwa da yammacin Larabar, fadar shugaban ta ce a shirye rundunar sojojin kasar take ta kai wa dakarun hari muddin ba su shiga taitayinsu ba.
- Sojoji sun hana shiga da fita a fadar Shugaban Kasar Nijar
- ECOWAS ba za ta lamunci juyin mulki a Nijar ba —Tinubu
Sanarwar dai ta biyo bayan rahotannin da suka yi ta yawo tun da safe cewa masu gadin fadar sun killace shugaba Bazoum a cikinta, sannan suka hana shi fita.
Lamarin dai ya sa an shiga fargaba cewar akwai yiwuwar a sami juyin mulki a karo na shida a kasashen Yammacin Afirka daga 2020 zuwa yanzu.
To sai dai a cikin wata sanarwa a shafukanta na sada zumunta, fadar shugaban ta ce, “Shugaban Jamhuriyar Nijar da iyalansa na nan kalau,” kodayake ba ta yi karin bayani ba a kan haka.
Sai dai daga bisani an goge sanarwar a daidai lokacin da ake ci gaba da zama a cikin halin rashin tabbas a kan ainihin abin da ke faruwa.
Gidan talabijin na kasar dai tun da rana yake saka kade-kade da wakoki.
Sauran sassan Niamey, babban birnin kasar kuwa, ko ina yayin tsit, amma mutane da ababen hawa na ci gaba da harkokinsu kamar yadda aka saba, in ji kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Tuni dai Shugaban kungiyar ECOWAS, kuma Shugaban Najeriya, bola Tinubu, ya ce kungiyarsu ba za ta lamunci duk wani yunkurin kifar da gwamnatin Dimokuradiyya ba a Nijar.