Ƙasar Faransa ta kora Belgium gida a Gasar Euro, bayan doke ta ci ɗaya mai ban haushi.
Faransa ta zura ƙwallo ɗaya tilo a wasan a minti na 85, bayan da ɗan wasan gabanta Kolo Muani ya yi ƙoƙarin jefa ƙwallo amma ɗan wasan bayan Belgium, Jan Vertonghen ya jefa ƙwallo a ragarsu.
- Lauyoyi mata sun nemi a samar da kotun sauraren shari’ar cin zarafi
- An soke aikin gyaran titi da aka ba kamfanin Dantata & Sawoe
Faransa, ta mamaye filin wasan na ‘yan 16 da aka buga a yammacin ranar Litinin.
Nasarar da zakarun Kofin Duniya na 2022 suka yi, ya sa sun kai matakin kwata final, wanda za su buga a ranar Juma’a mai zuwa.
’Yan wasan bayan Faransa, musamman Saliba ya yi ƙoƙari wajen hana ɗan wasan gaban Belgium Romelu Lukaku sakat a wasan.