Shugaban Jam’iyyar APC na riko Prince Hilliard Eta ya rantsar da Worgu Boms a matsayin Mataimakin Babban Sakataren Jam’iyyar.
Eta ya zabo Boms ne daga bangaren APC na jihar Ribas da Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar na kasa ya amincewa da shi.
Boms zai maye gurbin Victor Giadom wanda ya nada kansa matsayin shugaban jam’iyyar APC na riko a lokacin da Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyyar mai mulki. Matakin na Giadom ya yi sanadiyyar jam’iyyar ta takadar da shi tare da neman sa ya rubuta takardar ban hakuri a jaridu uku.
A lokacin da yake rantsar da Boms, Eta, wadda shi ne Mataimakin Shugaban APC na Kudu mai riko, ya ce Boms din zai ci gaba da gudanar ayyukansa na Mataimakin Sakataren Kasa na APC kamar yadda tsarin jam’iyya ya tanadar.
Idan za a iya tunawa, Giadom ya rubuta wa Hukumar Zabe (INEC) inda ya bayyana karara cewar bai nada wani kwamiti ba da zai gudanar da zaben fitar da gwanin takarar gwamnan Jam’iyyar APC ba a jihohin Ribas da Edo.
Wasikar na dauke da kwanan wata 18 ga watan Yuni, 2020 ya kuma raba wa jami’an tsaro.