Minista a Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje, Ambasada Zubairu Dada, ya yi wa jam’ar Jihar Neja alkawarin isar da kokensu ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Ambasada Dada, ya yi alkawarin ne a zamansa da masu ruwa da tsakin jihar domin cika umarnin Shugaban Kasa cewa kowane minista ya koma jiharsa ya tattauna da jama’a don jin kokensu.
- #EndSARS: A gaggauta kamo Nnamdi Kanu —Bayari
- Satar kayan tallafi: An samu gawar hudu a cikin dam
- Buhari ya yi alhinin mutuwar dalibai a hatsarin mota
Ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa, “Gwamnatin Tarayya na tare da ku, tana sane da matsalolinku, kuma za ta saurari koke-kokenku”.
Ministan ta bakin kakakinsa Ibrahim Aliyu ya yaba wa matasan na Jihar Neja da suka ki yin amfani da zanga-zangar #EndSARS wurin tayar da yamutsi a jihar.
Ya ce an kammala zaman da yammacin Alhamis kuma ya samu halarcin shugabannin addini, sarakuna, ’yan majalisar tarayya da na jihar, ’yan siyasa, mata da kuma matasa.
Ministan ya kuma gana da ayari daban-daban a jihar don jin bukatunsu ga Gwamnatin Tarayya.