✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

#EndSARS: Sojoji sun yi wa masu tayar da rikici kashedi

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta gargadi masu neman tayar da fitina a kasar da su shiga taitaiyinsu inda ta jaddada shirinta na kare kasar.…

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta gargadi masu neman tayar da fitina a kasar da su shiga taitaiyinsu inda ta jaddada shirinta na kare kasar.

Sanarwar da ta fitar a safiyar Alhamis ta yi kashedi ga masu neman kawo cikas ga tsarin dimokuradiyyar Najeriya cikas da su daina ko kuma su gamu da fushinta.

“Rundunar Sojin Kasa Najeriya na tabbatar wa ‘yan kasa na gari aniyarta ta tabbatar da aminci da tsaron mulkin dimokuradiyya a kasa.

“Tana kuma gargadin masu neman tayar da rikici domin a shirye take da ta kare Najeriya da kuma mulkinta na dimokuradiyya”, inji ta.

Sanarwar da kakakin Rundunar, Kanar Sagir Musa ya fitar na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da zanga-zangar ta neman yi wa rundunar SARS garambawul.

Idan ba a manta ba an samu wasu ba a san ko su wane ne ba sun kai wa masu zangar-zangar hari a Abuja da Legas da wasu sassan Najeriya.

Rundunar ta jaddada “mubaya’arta da Babban Kwamandan Tsaron Kasa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Kundin Tsarin Mulki.”

Sagir Musa ya kuma umarci dukkannin jami’an soji da kada su bari wani abu ya karkatar da su daga kare tsarin dimokuradiya a kasar.

Da yake bayani, Babban Jami’n Yada Labaran Rundunar Tsaro ta Kasa, Manjo Janar John Enenche ya ce masu kai wa masu zanga-zanga hari su ne masu neman tayar da rikici.