Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ce ma’ikatan jihar guda 25,000 sun kasa fita aiki sakamakon tare manyan hanyoyin zuwa Sakatariyar Jihar da masu zanga-zangar #EndSARS suka yi.
Gwamnan, yayin kaddamar da kwamitin binciken cin zarafi da zalunci da tauye hakkin da jami’an rusassiyar rundunar ’yan sandan SARS suka yi jihar ya bayyana takaicinsa kan kan rufe hanyoyin da ya hana ma’aikata da masu sana’o’i suka kasa zuwa wuraren neman abinci.
- Masu zanga-zanga sun tare hanyar Legas zuwa Ibadan
- Zanga-zangar #EndSARS za ta tsallaka Afirka ta Kudu
Ya ce, masu zanga-zangar na da hakki neman hakkinsu, amma kuma hakkin ’yan kasa ne da ke son gudanar da harkokinsu su ma a bar su su yi hakan ba tare da hantara ba.
Aminiya ruwaito cewar masu zanga-zangar sun rufe hanyoyi da dama a garin Legas, a wasu wuraren kuma har buga kwallon kafa su ke yi a kan titi.
Sanwo-Olu ya roki masu zanga-zangar da su bar mutane su fita zuwa wuraren ayyuka da sana’o’insu kamar yadda suka saba.
“Muna da mutane akalla miliyan 20 a nan”, kamar yadda ya ce.
Ya kuma bukace su da su janye zanga-zangar domin ba da damar warware matsalolin da ake da su a kasa.
“Hakan yana da amfani domin hana ’yan daba yi amfani da damar wajen aikata miyagun laifuka da suka shirya,” inji shi.
Ya bayyana kokarin da gwamnati ke yi na ganin ta saita hukumar ’yan sanda musamman a jihar Legas.
“Jihar Legas ba za ta taba bari a tauye hakkin wani mutu ba”, inji shi.
Ya kuma yi kira ga duk wani mutum da jami’an SARS suka musguna wa da ya gabatar da korafinsa a gaban kwamitin da aka nada don a bi masa kadi.