✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

#EndSARS: Gwamnati ta amsa bukatun masu zanga-zanga

Gwamnati ta umarci a saki dukkanin masu zanga-zangar da ake tsare da su

Kwamitin Shugaban Kasa na gyan aikin dan sanda ya yi zaman gaggawa inda ya amince da dukkannin bukatun masu zanga-zangar neman rushen sashen ‘yan sandan SARS masu yaki da ayyukan fashi.

Taron Kwamitin wanda aka kafa bayan rushe SARS ya ce masu zanga-zangar na da kwararan hujjoji don haka ya amince a saki dukkannin wanda aka tsare ba tare da sharadi ba sannnan a hana amfani da karfi a kan masu zanga-zangar.

“Sakamakon rushe SARS, zauren na kira da a dauki wadannan matakai nan take domin dawo da doka da kuma yardar ‘yan kasa ga ‘yan sanda:

“Shugaban ‘Yan Sanda ya ba wa dukkannin runuduninsa na jihohi umarnin dakatar da amfani da karfi a ka masu zanga-zanga; Sakin masu zanga-zanga da sauran ‘yan kasa ba tare da sharadi ba; tattaunawa da tuntubar ‘yan kasa domin ganin sun aminta da ‘yan sanda; da kuma bullo da hanyoyin aiwatar da rahoton Kwamitin Fadar Shugaba Kasa kan kan gyara aikin SARS,” inji sanarwar da mai magana da yawu shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar.

Karin bayani na tafe.