✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

#EndSARS: Buhari ya ba masu zanga-zanga hakuri

Fadar Shugaban Kasa na roko a kwantar da hankali tare da ba da tabbacin yin abin da ya dace

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ja hankalin masu zanga-zangar EndSARS da su kwantar da hankalinsu, a yayin da zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali a sassan Najeriya.

Buhari ya bayyana hakan ne ta hannun hadiminsa Femi Adesina a ranar Laraba.

“Fadar Shugaban Kasa tana rokon kowa ya kwantar da hankalinsa, sannan a fahimce ta domin ta shirya tsaf wajen kawo sauye-sauye ga Rundunar ’Yan Sanda tun daga matakin tarayya zuwa jihohi”, cewar Adesina.

Buhari ya jinjina wa gwamnatocin jihohi 13 da suka kafa kwamitin bincike na shari’a dangane da cin zarafin da ’yan sanda suka tare da ba da tabbacin gwamnatinsa za ta zartar da hukuncin da ya dace.

Zuwa yanzu jihohin da suka kafa kwamitin binciken sun hada da Legas, Kaduna, Delta, Ekiti, Ogun, Anambra, Inugu, Imo, Filato, Edo, Nassarawa, Ondo da kuma Akwa Ibom.

Shugaban ya ce tun asali yana da shirin yin sauye-sauye a hukumar ta ’yan sanda.

Sanawar na zuwa ne bayan tarzomar da ta kaure a ranar Talata a unguwar Lekki ta Jihar Legas, inda ake zargin sojoji da bude wuta a kan masu zanga-zangar #EndSARS.

Zanga-zangar dai ta dauki zafi tare da sauya fasali, a yayin da bata-gari ke cin karensu ba babbaka a wasu sassan na kasar nan.

%d bloggers like this: