Duk da dokar hana fita da Gwamnatin Jihar Adamawa ta saka, barayi sun fadada ayyukansu a jihar zuwa kamfanoni masu zaman kansu da ofisoshin gwamnati.
Bayan kwashe kayan abinci daga dakin ajiya na gwamnati a ranar Asabar, A ranar Litinin matasan sun kai samame a ma’ajiyar kungiyar manoma ta jihar, india suka yi awon gaba da taraktoci da injinan banruwa da buhunan takin zamani da irin shuka da sauran kayan amfani a yankin Kofare a birnin Yola.
Sun kuma sace shinkafar kungiyar manoma shinkafa ta RIFAN da ke Numan da sauran sace-sace a wurare da daman gaske a yankin na karamar hukumar ta Numan baya ga injinan aikin gona da suka sato daga ma’ajiyar kamfanoni masu zaman.
Matasan sun kai farmaki ma’adanar kamfanonin PZ da A.D. Basharu sannan suka auka wa Ofishin Ma’aikatar Lafiya ta jihar Adamawa, inda suka sace magunguna da kayan kula da lafiya da na ofis.
Shugaban Karamar Hukumar Numan, Innocent Koto, ya jagoranci tawagar karamar hukumar zuwa wuraren don shaida abun da ya faru.
Mun yi kokarin jin ta bakin Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandar Jihar, DSP Sulaiman Nguroje amma ba mu yi nasarar samun sa ba har lokacin da muke kammala hada wannan rahoton.