Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana gaban kwamitin binciken rikicin zanga-zangar #EndSARS da kwato hakkin wadanda aka zalunta na Jihar Legas.
Abin da ya fi daukar hankali shi ne zargin sojoji da harbin masu zanga-zangar a unguwar Lekki ranar 20 ga watan Oktoba, zargrin da sojoji suka sha musantawa.
- Harbin Lekki: Sojoji sun kawo bidiyon abin da ya faru
- An kubutar da matashi baya awa bakwai a cikin kwata
Amma lauyan rundunar, Akinlolu Keyinde, SAN, ya shaida wa kwamitin cewa babu ko takardar korafi daya da aka rubuta na zargin sojoji da harbin masu zanga-zangar #EndSARS a Lekki.
A shaidar da ya bayar, Kwamadan Rundunar Soji ta 81 Mai Binciken Kwakwaf, Birgediya Hameed Ibrahim Taiwo ya bayyana wa kwamitin cewa abin da rundunar ta yi bai saba ka’idar aikinta ba.
Ya ce rundunarsa ta yi aikin da doka ta dora mata ne bayan Gwamna Babajide Sano-Olu ya nemi agajinta a lokacin ‘yan daba suka kwace zanga-zangar suna kashe ‘yan sanda da kona dukiyoyin gwamnati da na jama’a.
Ya ce sabanin jita-jitar da ake yadawa, rundunar ta tura sojoji ne su kwantar da rikicin da ya bulla a fadin jihar bayan ta bayyana cewa kashe-kashen da kone-konen da ake yi ya fi karfin ‘yan sanda.
Birgediya Taiwo ya kuma haska wa zaman kwamitin na ranar Asabar bidiyon abin da ya faru daomin kafa hujja a kan abin da ya fada.
Ana iya tunawa tun da farko rundunar ta ce a shirye ta haska wa kwamitin bidiyon da ke tabbatar da cewa zargin da ake wa sojoji da harbin masu zanga-zanga a Lekki shaci-fadi ne.