Gwamnatin Jihar Ebonyi ta sassauta dokar hana fita da ta kakaba ta sa’o’i 24 don tabbatar da zaman lafiya yayin zanga-zangar #ENDSARS da aka yi a jihar.
Daga ranar Juma’a mutane a jihar za su kasance a gidajensu daga karfe 8:00 na dare zuwa karfe 8:00 na safe.
- Yadda jawabin Buhari kan #EndSARS ya tayar da kura
- Kasashe sun ba mu Dala 400,000 —Masu Zanga-zangar #EndSARS
- #EndSARS: Ba za mu zura wa mabarnata ido ba —Buhari
Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi ya bukaci mahukunta da hukummin tsaro da kuma ’yan jihar su yi kokarin kiyaye doka a matsayin ’yan kasa masu kishi da kuma kauce wa duk wani abu da zai iya janyo rikici a zanga-zangar wanda ka iya janyo asarar rayuka da dukiyoyi a jihar.
An sassauta dokar ne bayan kwana biyu yayin da wasu matasa suka yi yunkurin tayar da rikici lokacin zanga-zangar a wasu yankunan jihar.
Aminiya ta gano cewa, a yanzu haka an samu zaman lafiya a Abakiliki babban birnin jihar da kewaye.
An kuma bude shaguna sannan masu matocin sufuri da wasu cibiyoyi suna ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba.