✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malamai sun fara yajin aiki a Ebonyi

Yankunan da yajin akin ya shafa sun haɗa da: Ebonyi, Edda, Ezza South, Ezza North, Ivo, Ishielu da Ƙaramar Hukumar Ohaukwu.

Ƙungiyar Malamai ta Najeriya NUT reshen Jihar Ebonyi ta sanar da fara yajin aikin sai baba-ta-gani a ƙananan hukumomi bakwai na jihar sakamakon rashin biyan albashin watanni.

Yankunan da abin ya shafa sun haɗa da: Ebonyi, Edda, Ezza South, Ezza North, Ivo, Ishielu da Ƙaramar Hukumar Ohaukwu.

Ƙungiyar ta koka kan rashin biyan albashin sama da watanni uku ga malaman da ke Ƙananan hukumomin da abin ya shafa.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren ƙungiyar, Bassey Asuquo kuma aka rabawa manema labarai a Abakiliki babban birnin jihar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Bayan sanarwar da muka bayar a baya kan shirin fara yajin aikin, mun yi nazari sosai kan yadda shugabannin ƙananan hukumomi suka amince da biyan albashin mambobinmu.

“Ya zuwa ranar aiki ta Laraba, 5 ga Fabrairu, 2025, mun amince da cewa wasu ƙananan hukumomi sun biya albashin mambobinmu.

“Duk da haka, muna nadamar sanar da ku cewa shugabannin ƙananan hukumomi da dama sun gaza biyan kuɗaɗen albashin mambobinmu.

“A kan haka, an umurci dukkan mambobinmu na jihar da na reshen ƙananan hukumomin da abin ya shafa da su bi wannan umarni da kuma tabbatar da aiwatar da yajin aikin nan take daga ƙarfe 12:00 na daren ranar Alhamis 6 ga Fabrairu, 2025.