✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Emenike zai koma Chelsea

Duk da rashin zura kwallo a raga a gasar cin kofin duniya da ke gudana a halin yanzu a Brazil, dan wasan gaban Najeriya Emmanuel…

Duk da rashin zura kwallo a raga a gasar cin kofin duniya da ke gudana a halin yanzu a Brazil, dan wasan gaban Najeriya Emmanuel Emenike zai canza sheka daga kulob dinsa Fenerbahce da ke Turkiyya zuwa na Chelsea a Ingila kafin a fara kakar wasa ta bana.  Kakar wasa ta bana za ta fara ne a watan gobe (Agusta) idan Allah Ya kaimu.
Kafar sadarwar Dailymail ta Ingila ce ta kalato wannan labari a shekaranjiya Laraba. Ta ce tuni kulob din biyu suka cimma matsaya a kan canjin sheakar dan kwallon.  An ruwaito cewa kulob din Chelsea ya amince ya bai wa kulob din Fenerbahce zunzurutun Yuro miliyan 19 kwatankwacin Naira biliyan 4 da miliyan 300 don canza shekar dan kwallon.
Emenike dai ya zura kwallaye 12 daga cikin wasanni 28 da ya yi a gasar rukuni-rukuni na Turkiyya a kakar wasan da ta wuce.
Yana daga cikin ’yan kwallon da suka wakilci Najeriya a gasar cin kofin duniya da ke gudana a halin yanzu kuma Faransa ce ta fitar da Najeriya da ci 2-0 a ranar Litinin da ta wuce.