Mutumin da ya fi kowa kudi a duniya, Ellon Musk, ya yi amai ya lashe kan batun sayen kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kasar Birtaniya.
Hamshakin attajirin ya janye batun ne sa’o’i kadan bayan ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa zai sayi kungiyar, inda ya kara da cewa wata kungiyar wasannin da yake son saya.
- Salman Rushie Zai Iya Rasa Idonsa Bayan Harin Da Aka Kai Masa
- DAGA LARABA: Kayan mata: Gyaran jiki ko janyo cuta?
“Wasa kawai nake yi, amma babu wata kungiyar wasanni da zan saya. Amma da ina son saya, to tabbas Man U zan saya, domin tun ina dan karamin yaro suke burge ni,” inji shi bayan wani mai amfani da Twitter ya tambaye shi ko da gaske yake game batun sayen kungiyar.
An yi masa tambayar ce ba yan da farko ya wallafa cewa, “Zan sati Manchester United Manchester, barka,” amma bai yi karin haske ba.
Hakan kuwa na zuwa ne bayan wasu magoya bayan kungiyar da ba su ji dadin rashin katabus dinta ba a baya-bayan nan, sun bukaci Ellon Musk ta Twitter da ya saye ta.
Sun yi wa attajirin tayin ne a daidai lokacin da yake ficewa daga cinikin Dala biliyan 44 na sayen kamfanin Twitter, wata hudu bayan ya sanar da aniyarsa ta sayen kamfanin sada zumuntan da suka maka shi a kotu.
Ellon Musk dai ya yi fice wajen wallafa sakonni masu tayar da kura a Twitter, da yadda ba a iya bambance lokacin da yake wasa ko akasinsa.
A wani sako da ya wallafa kwana biyu bayan Majalisar Daraktocin Twitter ta amince da tayinsa na sayen kamfa, Musk ya rubuta cewa, “Nan gaba zan sayi kamfanin Coca-Cola domin a ci gaba da sanya gidan ibilis a ciki.”
Amma daga baya a ranar Laraba ya sake wallafawa a Twitter cewa “Kuma ba zan sayi Coca-Cola ba domin dawo da sanya hodar ibilis a ciki, duk da cewa akwai masu son hakan sosai.”