Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana jin dadinsa da sako daliban Jami’ar Greenfield da ’yan bindiga suka yi a yammacin ranar Asabar.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a shafinsa Twitter, inda ya yi wa daliban da iyayensu fatan alheri.
- Manyan masu laifi sun shiga hannu
- An ba da umarnin cafko wadanda suka kona caji ofis a Imo
- An sake kone ofishin ’yan sanda a Imo
“Gwamnatin Kaduna na maraba da sako daliban Greenfield. Tana yi musu fatan warwarewa daga ukubar da suka sha a hannun ’yan bindigar, tare da jajanta wa wadanda suka rasa rayukan ’ya’yansu.
“Gwamnatin Kaduna na shirye-shirye tare da Gwamnatin Tarayya da sauran hukumomin tsaro don ganin yadda za a ceto mutanen da ’yan bindiga suka sace,” kamar yadda ya wallafa.
Tun a watan Afrilu ’yan bindiga suka kutsa cikin Jami’ar Greenfield da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja suka yi awon gaba da dalibai da wasu ma’aikatan jami’ar.
Wasu rahotanni na nuni da cewa sai da iyayen daliban suka biya kudin fansa sannan masu garkuwar suka aminta tare da sako su a ranar Asabar.