Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid da Barcelona za su kara a gasar Super Cup a kasar Saudiyya.
Wannan ita ce shekara ta biyu da kasar Saudiyya take daukar nauyin gudanar da gasar.
- AFCON 2021: Najeriya ta yi wa Masar ci 1 mai ban haushi
- Kasar Girka ta ba wa Najeriya tallafin rigakafin COVID-19
Kungiyoyin biyu za su barje gumi ne a ranar Laraba da misalin karfe 8 na dare.
Atletico Madrid kuma za ta kara da Athletic Bilbao a ranar Alhamis.
Kowane wasa zai kasance daga shi sai wasan karshe na Gasar ta Super Cup.
A shekarar da ta wuce Real Madrid ce ta yi nasara lashe kofin, inda ta doke Atletico Madrid a bugun fenareti.
Sai dai masu hasashe kan harkokin wasanni na ganin Real Madrid za ta iya nasara a kan Barcelona, duba da irin matsalolin da Barcelonar ke fuskanta a bana.