✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta tsare ‘yan damfarar intanet 9 a Abuja

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, EFCC a yau Laraba ta ce, ta tsare wasu ‘yan damfarar intanet 9…

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, EFCC a yau Laraba ta ce, ta tsare wasu ‘yan damfarar intanet 9 da aka fi sani da Yahu-yahu a babban birnin tarayya Abuja.

Wani sashi da ke aikin bankado  ‘yan damfara na hukumar EFCC ne suka gano wadanda ake zargin tun ranar 30 ga Nuwamba 2018 kamar yadda mukaddashin kakakin hukumar EFCC Tony Orilade ya sanar.

Sunayen wadanda aka tsaren sun hada da: Edwin Ogbomwan, Okouromi Franklin, Oseji Collins, Collins Onyekwuluje, Anyanechi Ekene, Tony Oviasuyi, Chidi Emeshili, Osaigbovo Aiseos da Osaigbovo Ikponmnosa.