Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya ce sun damu nasarar kwato makudin kudi kimanin Naira biliyan 511.9 a shekarar 2017.
Shugaban hukumar na riko ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bayanin kasafin kudin hukumar a gaban kwamitin da ke lura da harkokin yaki da cin hanci na Majalisar Wakilai karkashin jagorancin Kayode Oladele.
Ibrahim Magu ya kara da cewa hukumarsa ta kwato kimanin Naira biliyan 473 da dala miliyan 98, da fam miliyan 7 da fam dubu 284 da dai sauransu duk a bara.