Jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) sun damke wata mata a ranar Asabar da ake zabe dauke da katin zabe guda 18 da kuma jerin sunayen masu zabe a Jihar Kaduna.
Matar ta shiga hannu ne a yankin Badarwa, inda EFCC ta bayyana hoton matar da ma katinan zaben da aka kama ta da su.
EFCC ta ce jami’anta sun cafke matar ce tana dauke da wata takarda mai shafi 17, cike da sunayin masu zabe da kuma bayanan asusun bankinsu da lambobin waya a Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa.
Hukumar ta ce matar ”’yar daya daga cikin manyan jam’iyyun siyasa a Jihar Kaduna ne,” kuma ta shiga hannu ne bayan jami’an hukumar sun dana mata tarko a matsayin masu zabe da ke son sayar da katin zabensu.
“Tana can tana amsa tambayoyin a ofishin EFCC da ke Kaduna, domin cafko abokanta da suke harkar sayen katin zabe da biyan kudi ta PoS,” in ji hukumar.
Gabanin zaben na ranar Asabar, an samu rahotannin kama mutane da tarin Katin Zabe a lokuta daban-daban wadanda alamu suka nuna an tanade su ne domin tafka magudi yayin zabe.
Ko a baya-bayan nan, an tsinci tulin katin zaben da ba a fayyace adadinsu ba a daji a Jihar Anambra.
INEC ta sha gargadin cewar, mallakar tulin katin zabe shirme ne, saboda ko an mallake su din ba za a iya amfani da su wajen zabe ba saboda kyakkyawan shirin da ta yi wa zaben.