✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC na neman hadimin Tambuwal kan damfarar N2.2m

Ana zargin hadimin gwamnan da damfarar wasu dillalan motoci N2.2m.

Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) na neman wani hadimin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato kan sha’anin tsaro, Bello Malami Tambuwal, bisa zargin damfarar kudi Naira miliyan 2.2.

Shugaban shiyyar jihar na hukumar, Usman Kaltungo, ya ce hadimin na musamman na amfani da mukaminsa wajen damfarar dillalan motoci.

  1. NUJ ta rantsar da sababbin shugabanni a Gombe
  2. Matashi ya kone kansa saboda ya gaza biyan kudin jarrabawa

“Yana zuwa wajen dillalan motoci yana yi musu zamba cikin-aminci.

“Yana fada musu cewar gwamna ne ke son saya wa wani mota,” a cewar Kaltungo.

Ya kara da cewa galibin motocin da hadimi ya damfara kirar Hyundai ne.

“Idan ya karbi motocin yana sayar da su ya yi amfani da kudin a wani abin,” a cewarsa.

A cewar Kaltungo, hadimin gwamnan da za a gurfanar a ranar Alhamis, ya sha fadawa cikin rikici iri-iri ana yin belinsa.

Ya ce tuni aka samu kudi Naira miliyan 1.6 a hannunsa, ban da Naira miliyan 2.25 da ake nema a wajensa.