✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duniya ta taru domin ban kwana da Mandela

Shugabanni daga kasashen duniya daban-daban ne suka hadu da dubun dubatan ‘yan Afrika ta Kudu a babban filin wasa na Soweto inda aka gudanar da…

Shugabanni daga kasashen duniya daban-daban ne suka hadu da dubun dubatan ‘yan Afrika ta Kudu a babban filin wasa na Soweto inda aka gudanar da taron addu’a domin ban kwana da marigayi tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela.
Marigayi Nelson Mandela ya rasu ne a ranar Alhamis yana da shekara 95, bayan jinya day a yin a wadansu watanni. Tun da ya rasu ake ta gudanar taron tunawa da shi kafin a binne gawarsa jibi Lahadi.
A jawabinsa, Shugaban Amurka Barack Obama ya ce duniya ta yi rashin da ya fi kowanne. Yana mai kwatanta Nelson Mandela da cewa mutum ne da babu kamarsa a karni na 20 wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen kwato ‘yancin jama’a.
Ya ce, Nelson Mandela ya koyar da duniya yadda karfin aiki da kuma karfin kyawawan tunani suke tasiri, kuma Mandela ba kawai wadanda aka daure ya kwance ba, har mai daurewar ya ‘yantar da shi.
Shugaba Obama ya yi juyayin cewa, ‘’ ba za mu sake ganin mutum kamar Nelson Mandela ba, mutumin da ya taimaka mini na zama mai sha’awar zama mutumin kirki.’’
A lokacin da yake hawa dandamalin rumfar manyan baki, shugaba Obama ya yi hannu da shugaban kasar Cuba, Raul Castro, wani abu da ba a taba gani ya faru ba a tsakanin shugabannin kasashen biyu saboda rashin jituwar da ke tsakanin kasashen biyu sama da shekaru hamsin.
A nasa jawabin, shugaban kasar Cuba Mista Raul Castro ya bayyana marigayi Nelson Mandela a matsayin wata alama ce ta dattako da kuma gwagwarmayar juyin jiuya hali.
A zamanin mulkin yayansa Fidel Castro, kasar Cuba ta kasance a sahun gaba wajen sukar nuna wariyar launin fata kuma Nelson Mandel ya yi matukar yabawa da wannan goyon bayan da kasar ta ba su.
Shi kuwa a nasa jawabin, Sakatare janar na Majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon cewa ya yi ana juyayin babban rashi kuma ana murnar wanda ya yi rayuwa mai amfani.
Ya ce, kasar Afirka ta kudu ta yi rashin jarumin gwarzo kuma ta rasa uba. ‘Yana daya daga cikin manyan malamanmu, wanda yake koyarwa ta hanyar nuna kyakkyawan misali, ya sadaukar da ransa kuma a shirye yake ya bayar da komai nasa domin tabbatar da ‘yanci da kuma mulkin damokaradiyya.
A yayin gudanar da addu’a a cocin Methodist da ke Johannesburg, Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu ya shawarci ‘yan kasar Afirka ta Kudu ne cewa kada su manta da ayyukan kirkin da Mandela ya gabatar a rayuwarsa.
Mista Zuma ya jinjina wa Mandela saboda namijin kokarin da ya yi wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da sansantawa, ‘ya yi tsayin-daka wajen tabbatar da ‘yanci, ya yaki wadanda ke zaluntar wadansu, yana so kowa ya samu ‘yanci.’’
A Cape Town kuma, Archibishop Thabo Makgoba cewa ya yi, Mandela babban manuni ne da ke nuna wa mautane cewa mutane suna da ikon sauya al’amura a duniya.
A cocin katolika na Mundi da ke Soweto kuma, Limamin cocin Sebastian Roussouw cewa ya yi,marigayi Nelson Mandela ya kasance ‘’haske ne a lokacin duhu.’’
An ci gaba da gudanar da addu’o’i a kasar Afirka ta kudu na tsawon kwanaki uku a kasar. Shugabannin kasashen duniya da dama ne, ciki har da Dilma Rousseff na Brazil da Raúl Castro Ruz na Cuba da Firaministan Birtaniya, Dabid Cameron da na Najeriya Jonathan Goodluck suka halarci taron addu’ar ban kwana da marigayi Nelson Mandela.
 An ajiye gawar Nelson Mandela a cikin ginin Union Buildings na Pretoria, inda aka rantsar da shi shugaban kasar Afrika ta Kudu bakar fata na farko a shekarar 1994. An dauko akwatin gawar da aka nade da tutar kasar ne a keken doki, inda ‘yan sanda suka yi mata rakiya kan Babura, yayin da jiragen helikopta ke shawagi a kan su.
Dakarun soji ne suka shigar da gawar cikin ginin na Union Buildings. Za a bar gawar ta Mandela a cikin ginin ne zuwa kwanaki uku. A ranar Lahadi  kuma za a binne gawar a kauyen kunu da ke Afrika ta Kudu.

Muna tare da shi har lokacin da ya cika   -‘Yarsa
Makaziwe ‘yar marigayi Nelson Mandela ce, ta bayyana wa BBC cewa, matar mahaifinsu Graca da ‘ya’yansa da jikokinsa suna tare da shi har lokacin da ya cika.
Ta bayyana cewa, ‘ Graca tana nan, ‘ya’yansa suna nan, jikokinsa suna nan, kowane lokaci muna tare da shi har zuwa lokacin da ya cika, muna tare da shi duk tsawon ranar Alhamis.’
Ta ce, ‘’ ina ganin daga ranar Jumu’a zuwa ranar Alhamis day a rasu, zan iya cewa lokaci ne mai ban mamaki, domin lokaci ne da za a iya cewa na shirye-shiryen ban kwana da duniya ga Tata (Nelson Mandela), kuma bai nuna wata damuwa ba saboda muna tare da shi.’’
‘’ Lokacin da likita ya bayyana mana, ina zaton a ranar Alhamis ne cewa, babu abin da za su iya yi, sai ya fada mini cewa in kira duk wadanda suka zo gaishe da ke wurin zai yi ban kwana da su, wata rana ce mai ban mamaki a gare mu.’’
Makaziwe ta yaba wa likitocin asibitin da Mandela ya kwanta saboda kyakkyawar kulawar da suka ba mahaifinsu dare da rana.

Aurensa da matar tsohon shugaban kasar Mozambic
Nelson Mandela ya yi aure har sau uku a rayuwarsa, matarsa ta farko ita ce Ebelyn Ntoke Mase wadda ya aure ta a garinsu Transkei a shekarar 1944, ita ‘yar uwar Walter Sisulu ce. A littafin rayuwarsa da ya rubuta da hannunsa mai taken: ‘’Doguwar tafiyar neman ‘yanci’’, ya bayyana cewa, a shekarar 1955 ce matarsa Mase ta bukaci ya zabi daya a tsakanin ita da kuma jam’iyyar ANC, domin saboda gwagwarmayar da yake yi ya kasa samun jituwa a tsakaninsa da matarsa Mase, a karshe dai dole ya rabu da ita. Suna da ‘ya’ya biyu maza.
Mandela ya kuma auri Winni Madikizela a shekarar 1958, amma auren ya rabu a shekarar 1996. Suna da ‘ya’ya mata guda biyu, wadanda suka girma lokacin da aka tsare mahaifinsu a shekarar 1962 a tsibirin Robben.
Nelson Mandela ya auri Graca Machel, matar tsohon shugaban kasar Mozambic Samora Machel a shekarar 1998, lokacin yana da shekara 80.
Da take yi wa manema labarai bayani a shekarar 2007, Graca ta bayyana cewa,’’ dukkanmu muna fama da zaman kadaici wanda ya sanya muke bukatar wanda za mu rika magana da shi, wanda kuma zai fahimce mu. Da farko na yi rantsuwa ba zan sake yin wani aure ba, amma sai ya ba ni mamaki ya sanya ni na sake shawara.’’

An kiyasta cewa shugabannin kasashe 91 da tsofaffin shugabanni guda 10 ne suka halarci addu’ar Mandela. Ga kadan daga cikinsu:
1. Dabid Cameron na Ingila
2. Barack Obama na Amurka
3. François Hollande na Faransa
4. Ban Ki-moon, Sakatare Janar na Majalisar  dinkin Duniya
5.  Angela Merkel ta Jamus.
6. Tony Abbott Firayiministan Australiya
7. José Manuel Barroso, Shugaban EU Commission
8. King Willem Aledander na Netherlands
9.  Yarima mai jiran gado Felipe da Firayiminista Mariano Rajoy na Spain.
10. Dilma Rousseff na Brazil
11. Mahmoud Abbas na Palestin
12. Pranab Mukherjee na Indiya
13. Robert Mugabe na Zimbabwe
Tsofaffin shugabannin kasa
1. Gordon Brown  
2. Tony Blair
3. Sa John Major,
4. Bill Clinton
5.  Jimmy Carter,
6. George W.Bush