Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya ce kowanne takun kasa daya a jiharsa garkuwa ne daga annobar COVID-19.
Idan za a iya tunawa, a baya gwamnan ya tsaya kai da fata cewa sam babu cutar a jihar, inda ya gargadi wadanda ya kira masu neman kudi da ita da su daina ko su hadu da fushin Ubangiji.
- 2023: Kungiyar Arewa ta dage kan lallai sai Yahaya Bello ya tsaya takarar Shugaban Kasa
- Ramadan: Shin dole ne Najeriya ta bi lissafin Saudiyya?
Gwamnan ya ba da tabbacin da kuma gardagadin ne a Lokoja yayin da yake kaddamar ayyukan Gwamnatin Tarayya na dibar ma’aikata 774,000 domin rage radadin annobar a jihar.
Yahaya Bello ya kuma koka kan ayyukan wasu wadanda ya yi zargin sun kirkiro kwayar cutar ne domin su ci gaba da mayar da wasu kasashe saniyar tatsa, yana mai cewa shi bai taba yarda ma akwai ta ba.
Ya zargi wasu jami’an gwamnati da amfani da ita a matsayin hanyar zurarewar kudade daga lalitar gwamnati wadanda ya kamata a yi amfani da su wajen ayyukan raya kasa, yana mai cewa ya ki ya bi inna-rididi wajen kasuwanci da cutar.
Yahaya Bello ya ce, “Tun da cutar HIV/AIDS ta bulla a shekarar 1985 duk da irin illar da take yi wa dan Adam, har yau an kasa samo maganinta, abin da kawai suka iya yi shi ne gano magungunan da ke dakushe kaifinta.
“Me ya sa cikin kasa da shekara daya da bullar COVID-19, China da kasashen yamma suke rige-rigen samo maganinta? Ai mutum ba ya bukatar wani boka ko dan duba ya fada masa cewa zallar siyasar duniya ce kawai ake bugawa da ita.
“Ba zan hana duk wanda yake son rigakafin ya je a yi masa ba, amma shawarata gare shi ita ce ya kamata ya farga, kuma ina masa fatan alheri,” inji Yahaya Bello.
Ya ci gaba da cewa, “A bara, akasarin jihohi sun kasance cikin dokar kulle na tsawon watanni.
“Mutane da dama sun mutu saboda yunwa a kan kwayar cutar da duk wanda ya kamu da ita yake da damar warkewa da kaso 95 cikin 100 ba tare da ya sha kowanne irin magani ba. Wannan ne dalilin da ya sa na ki yarda in kulle jihata.
“Ina gargadin wadanda ke fakewa da COVID-19 suna wawure kudaden gwamnati da su daina tun kafin fushin Allah Ya same su.
“Saboda haka ina kira ga jihohi da hukumomin gwamnati da ma daidaikun mutane da ke fama da cutar COVID-19 da su kawo masu fama da ita jihar Kogi; ina mai tabbatar muku da zarar motar da aka dauko su ta shigo kasar jihar Kogi za su warke nan take, mu kuma su rika biyan mu.
“Da irin wadannan kudaden za mu iya inganta harkar lafiya da ma sauran ayyukan raya kasa a jiharmu,” inji gwamnan.