Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa, INEC ta bayyana cewa za ta zuba idanu tare da jami’ai sosai domin tabbatar da cewa babu wani dan siyasa ko dan koren ‘yan siyasar da ya je rumfunan zabe dauke da kudade ya na rabawa a lokacin zaben gwamnan Ekiti wanda za a yi ranar 14 ga Watan Yuli na wannan shekara.
Shugaban Hukumar Zabe, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi wannan gargadi ne a wurin wani taron masu ruwa da tsaki a kan aikin Cigaba da Rajistar Zabe a Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti a farkon wannan makon. Ya mai cewa hukumar tasa za ta hada karfi da jami’an tsaro domin ta tabbatar ta hana dukkan wata harkalla ta sayen cinikin masu jefa kuri’a a ranar zabe a rumfunan zabe.
Ya ce duk wanda aka kama ya na watandar kudade a rumfunar zabe ko a ranar zabe, to zai dandana kudar hukuncin da mai shari’a zai yanke masa.
Farfesa Yakubu ya yi matukar nuna bacin ransa bisa ganin irin yadda aka yi amfani da tsabar kudi a lokacin zabukan gwamnonin jihohin Edo, Ondo da Anambara, ta yadda wasu har naira dubu biyar-biyar su ka rika rabawa.
Taron dai ya samu halartar Mataimakin Gwamnan Jihar Ekiti, wanda kuma shi ne dan takarar zaben gwamna na Jam’iyyar PDP da sauran wasu shugabannin jam’iyyun siyasa, jamai’an tsaro, kungiyar mata ‘yan kasuwa ta jihar da kungiyoyin sa kai da sauran su.
Shugaban Zabe na Shiyyar Oyo da Ekiti da Osun da kuma Ondo, Farfesa Prince Addeji Soyebi ne ya wakilci Shugaban Zabe na kasa. Inda ya sake jaddada cewa “Ba za mu bari kowace mota ta matsa kusa da rumfar zabe ba, saboda ‘yan siyasa kan boye kudade a cikin mota. Ta haka ne za mu iya rage yadda ‘yan siyasa ke yawo da kudi niki-niki a cikin aljifansu.”