Wata sabuwar dambarwa ta dabaibaye aikin gina gadar sama a Kofar Dan Agundi da Gwamnatin Kano ta kaddamar.
A ranar Juam’a ne Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da aikin Gadar Tal’udu a kan biliyan 14.45 da kuma Gadar Dan Agundi wanda za a aiwatar a kan kudi Naira biliyan 15.9 a bisa tsarin hadaka tsakanin kananan hukumomi da matakan gwamnatin jihar.
Gwamna Abba ya bayyana cewa ayyukan biyu za su kawo bunkasar arziki a jihar da kuma rage cunkoson ababen hawa a yankunan da aka sanya gadoji.
Gwamnan ya kaddamar da aikin ne bayan wata Kotun Tarayya ta hana gwamnatin jihar amfani da kudin kananen hukumomi a aikin.
- Dauda Lawal ya gwangwaje ma’aikatan Zamfara da albashin wata guda
- Dalilan da Hafsat Chuchu ‘ta kashe’ Nafi’u
Kotun da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin wucin gadin ne bayan shugabannin kananan hukumomin jihar 44 sun yi karar gwamnatin jihar suna neman a hana ta amfani da kudadensu a aikin.
Aminiya ta gano cewa a ranar Alhamis ne kotun ta ba da umarnin, Juama’a kuma Gwaman Abba ya kaddamar da aikin wanda aka ba wa kamfanin CGC Nigeria Limited.
Kawo yanzu dai gwamnatin Kano ba ta ce komai ba game da umarnin kotun.
Gwamnatin Kano ta tsara cewa za a biya kashi 70 cikin 100 na kudin aikin ne daga asusun Kananan hukumomin jihar 44, a yayin gwamnatin jihar za ta biya ragowar kashi 30.
tuni dai Majalisar Zararwar Jihar Kano ta umarci Ma’aikatar Kudi ta ba wa CGC Nigeria Limited kafin alkalami na Naira biliyan 6.38 domin fara aikin.
Naira biliyan 1.91 daga cikin kudin kafin alkalamin za a fitar ne daga asusun jiha, biliyan 4.37 kuma daga asusun kananan hukumomi.
tsarin yaddda za a biya dukin aikin dai a jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu ke cewa bai dace ba a dauki kudaden wasu kananan hukumomi a sanya a aikin da ba su za a yi wa ba.
Sai dai kuma wasu na ganin aikin na da muhimmanci ganin yadda gadojin biyu za su kawo cigaba da kuma saukake cunkoson ababen hawan da ake samu a yankunan biyu.