✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilan da Hafsat Chuchu ‘ta kashe’ Nafi’u

Makwabtan su Hafsa sun ce tsohon saurayinta ne a yayin da mahaifin Nafi'u ke diga alamar amabaya kan yadda ita kadai za ta iya kashe…

Tun lokacin da Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta ba da sanarwar kama wata mata mai suna Hafsat Sani Suraj wadda aka fi sani da Chuchu bisa zargin kashe wani mai suna Nafi’u Hafizu dan Jihar Bauchi ake ta samun bayanai masu cin karo da juna game da alakarta da marigayin da kuma dalilin yin kisan.

Da farko ’yan sanda sun bayyyana marigayi Nafi’u da cewa yaron mijin Hafsat ne, sai kuma mutanen gari suka bayyana shi da direban gidan, yayin da wasu suka bayyana shi a matsayin abokin kasuwancinta, sannan mahaifin marigayi ya bayyana cewa abokin kasuwancin mijin matar ce.

Sai dai binciken da Aminiya ta gudanar a Layin Isa Dagwanje da ke Unguwa Uku, a birnin Kano, inda nan ne mahaifar wacce ake zargi, Hafsat Suraj Chuchu, ta gano cewa marigayin tsohon saurayin Hafsa ne wanda daga baya suka kulla alakar kasuwanci tare.

Majiyarmu ta ce da wannan alaka ta kasuwanci masoyan suka kwashe lokaci suna ci gaba da gudanar da boyayyiyar soyayyarsu inda hatta mijinta ya gaza fahimtar halin da ake ciki ballanatana ya dauki matakin raba tsakanin masoyan boyen.

Ainihin alakar Hafsa da Nafi’u —Makwabta

Wani matashi da ya bayyana sunansa da Dagwanje kawai, ya bayyana wa Aminiya cewa Nafi’u tsohon saurayin Hafsat ne wanda Allah bai yi aure a tsakaninsu ba, inda iyayenta suka bayar da ita ga daya daga cikin malaman Islamiyyarta.

“A gaskiya mun san cewa Nafi’u saurayinta ne. Akwai wani lokaci ma da ta bar gida har aka rika cewa ta bata, to a wancan lokacin ana tunanin wurinsa ta je.

“To lokacin da iyayenta suka fuskanci ta fara fitina sai suka aurar da ita ga daya daga cikin malaman Islamiyyarsu, Dayyabu Abdullahi,” in ji shi.

Ya ce bayan Hafsat ta yi aure daga baya sun sake kulla alaka da Nafi’u inda suka zama suna zaune a gida daya.

“Mu dai ba mu san yadda aka yi suka sake kulla alaka ba, sai dai kawai bayan ta yi aure muka fuskanci cewa suna tare da Nafi’un.

“Domin muna yawan ganin sa yana zuwa gidansu wajen iyayenta. Ko kuma mu gan su tare a mota da sauransu.

“Daga baya sai ake gaya mana cewa wai a yanzu kasuwanci suke yi tare har ma sun bude shaguna a wurare daban-daban,” in ji shi.

‘Nafi’u ne ya gina gidan da suke ciki’

Dagwanje ya shaida wa Aminiya cewa shi kansa gidan da su Hafsat suka tare a ciki kimanin shekara daya da wasu watanni Nafi’un ne ya gina shi.

Ya ce, “Ba na tantama cewa wannan gida da suka tare a ciki marigayin ne ya gina shi. Domin lokacin da ake aikin ginin gidan na sha ganin Nafi’u yana biyan ma’aikata kudin aikinsu da kuma kaiwa da komowa wajen abin da ya shafi ginin gidan.

“Abokina ne ma ya yi aikin silin din gidan. Wata rana na je wurinsa a gabana marigayi Nafi’u ya biya shi wasu kudi.”

A cewar majiyar, marigayi Nafi’u ya yi niyyar ci gaba da zama tare da su Hafsat a gidan idan ya yi aure inda shi zai zauna a saman gidan yayin da ita kuma da mijinta za su ci gaba da zama a kasan gidan.

Majiyar ta ce dangantaka ta yi tsami a tsakanin Hafsat da marigayi Nafi’u ne bayan da marigayin ya yunkuro zai yi aure.

“Tun daga lokacin da marigayi Nafi’u ya dauko batun aure, shi ke nan aka fara samun zaman doya da manja a tsakaninsu, inda har a karshe ake zaton wannan rigimar ce ta kai Hafsat ga daukar matakin kisan marigayin,” in ji majiyar.

Mun dauka shi ne mijinta —Makwabta

Har ila yau Aminiya ta kai ziyara gidan da ake zargin ta gudanar da wannan aika-aikar a ciki da ke Layin ’Yan Awaki a Unguwa Uku, inda ta samu bayanan cewa kasancewar Hafsat ba ta dade a unguwar ba kuma ba ta kula mutanen unguwar don haka ba su san komai a kan rayuwarta ba.

Wani makwabcin gidan ya shaida wa Aminiya cewa, “Tun da suka tare a gidan tsawon shekara daya da watanni ba su yin mu’amala da mutanen unguwa, don haka ba mu san komai game da abin da suke ciki ba.

“Gara ma shi marigayin muna ganin sa yana dan fitowa kofar gida ya zauna har ya yi wasa da yaran unguwa.

“Amma ita muna ganin fitarta ko dawowarta a cikin mota. Shi kuwa mijinta ma ba mu san shi ba. Domin mu wallahi sai da wannan lamarin ya faru sannan muka san cewa ba shi ne mijinta ba. Saboda ba mu taba ganin mijin ba.”’

Har ila yau binciken Aminiya ya gano cewa marigayi Nafi’u ba yaron mijin Hafsat ba ne ko direba kamar yadda ake ta yayatawa ba.

Dagwanje ya ce, “Gaskiya dama marigayi Nafi’u dan kasuwa ne yana kasuwancin tufafi a Kantin Kwari.

“Daga baya ya fadada kasuwancinsa zuwa harkar magungunan asibiti da lemo da sauransu.

“Idan ma har batun yaro ake yi to sai dai mijin Hafsat din wato Malam Dayyabu ya zama yaron marigayin. Domin shi marigayin ne ma ya buda wa Dayyabun harkokin da yake yi a Kantin Kwari.”

‘Mun dauka ma’aurata ne’

Aminiya ta kai ziyara a wani shago da Hafsat take gudanr da kasuwancin dogwayen rigunan mata (abaya) da turare, mai suna “Chuchu Fashion” da ke rukunin shagunan zamani na ALHAMSAD TOWER a Titin Gidan Zoo inda makwabtan shagon wadanda ke sana’ar dinki suka ce iya tsawon saninsu da marigayin da Hafsat ba su taba tunanin ba ma’aurata ba ne.

“Mu wallahi mun dauka ma’aurata ne. Dama tun da suka fara zama a shagon wani lokaci ita take zama wani lokacin kuma shi marigayin ne ke zama. A wani lokacin kuma za ka same su tare a shagon.

“Daga baya ne suka samo wata yarinya take kula musu da shagon. To mu ba mu taba zaton ba ma’aurata ba ne sai yanzu da wannan lamari ya faru,” in ji su.

Hafsa na da cutar aljanu —Mahaifiyarta

Yayin da Aminiya ta kai ziyara gidan iyayen Hafsa ta iske mahaifiyarta Hajiya Hajara Suraj, inda ta ce ba za ta iya yin magana mai tsawo ba saboda rashin lafiya da take fama da ita.

“A yanzu haka ma magani na sha ina fama da rashin lafiyar da ta shafi zuciya da hawan jini.

“Dama can ba ni da lafiya to kuma da wannan abu ya faru sai jikina ya kara rikicewa don haka ba zan iya yin magana mai tsawo ba,” in ji ta.

Sai dai ta shaida wa Aminiya cewa abin da ta sani tsakanin Hafsa da Nafi’u abokan kasuwanci ne.

“Abin da na sani shi abokin kasuwnacinta ne. Kuma ban san abin da ya faru ba sai waya aka yi min aka sanar da ni. Da muka je muka ga gawar. Daga nan ban sake sanin abin da ake ciki ba,” in ji ta.

Ta ce Hafsat ’yarta tana fama da cutar aljanu tun tana yarinya. “Dama can yarinyar nan kowa ya san tana fama da iskokai. Suna kuma tasar mata lokaci-lokaci. Kowa ya san haka a unguwar nan.

“Ko a makarantarsu ta Islamiyya da ta sakandare malamanta da daliban da suka yi karatu tare sun san haka. In takaice miki ma tana zuwa asibitin masu kula da kwakwalwa tana karbar magani,” in ji ta.

Ina da shakku —Mahaifin Nafi’u

A tattunawar Aminiya da mahaifin marigayi Nafi’u, Alhaji Hafiz Gorondo ya ce yana shakku game da yadda za a ce Hafsat ita kadai ta kashe dansa, inda ya yi kira ga ’yan sanda su tsananta bincike don gano yadda aka yi kisan.

“Ina mamakin yadda za a yi wannan ’yar karamar yarinyar ta iya kashe Nafi’u haka kawai, duba da yanayin jikinsa da yadda yake da karfi,” in ji shi.

Mahaifin ya ce dan nasa ya shaida masa cewa akwai batun kudi a tsakaninsa da mijin matar, kuma yadda mijin ya shaida masa cewa ya rasu ne sakamakon jinyar da ya yi a wani asibiti da kuma yadda ya ji makanikensa ya ce ya yi ta nemansa tun karfe 11 na safe ya je ya dauki motarsa amma bai same shi a waya ba ya sa ya fara zargin ba mutuwar Allah da Annabi Nafi’u ya yi ba.

Kuma ya ce wannan ne ya sa ya nemi a bude gawarsa, inda suka ga alamun inda aka sossoke shi da wuka a wurare da dama.

Shigar ’yan sanda cikin lamarin

A ranar Asabar ce ’yan sandan Jihar Kano suka kama Hafsat bisa zargin kisan Nafi’u Hafiz a Unguwa Uku.

Wata sanarwa dauke da sa hannun Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Haruna Kiyawa ta ce matar ta yi amfani da wuka wajen caccaka wa marigayin a wurare daban-daban a jikinsa lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Hafsat ta dauki alhakin aiwatar da kisan inda ta ce ta kashe shi ne lokacin da yake kokarin hana ta kashe kanta.

’Yan sanda sun kama mijin Hafsat mai suna Dayyabu Abdullahi da limamin da ya yi masa wanka.

An gurfanar da Chuchu a kotu

A shekaranjiya Laraba ne aka gabatar da Hafsat a gaban Babbar Kotun Majistare da ke ’Yankaba a Kano bisa zargin ta da kisan Nafi’u.

Mai gabatar da kara Lauyan Gwamnati Barista Lamido Sorondinki ya shaida wa kotun cewa ana tuhumar matar da laifuffuka biyu na yunkurin kisan kai da yi wa wani kisan gilla, laifuffukan da suka saba da sassa na 281 da 221 na Kundin Final Kod.

Barista Lamido Sorondinki ya ce wacce ake zargi ta yi amfani da wuka don kashe kanta inda ta yanka hannunta na hagu, “A wannan lokaci ne ta yi amfani da wannan wuka ta daba wa Nafi’u Hafizu a kahon zuciya lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarsa”

Wacce ake zargin ta amsa laifinta na farko yayin da ta musanta laifi na biyu.

Alkalin Kotun Mai shari’a Hadiza Abdurrahman ta ba da umarnin a tsare wadanda ake zargi a gidan gyaran hali tare da dage shari’ar zuwa ranar 1 ga watan Fabrairun 2024.

Mijin Hafsa da maigadi a gaban kotu

Har wa yau an gurfanar da karin mutum uku da suka hada da mijin Hafsat, Dayyabu Abdullahi da Adamu Muhammad da Nasidi Ibrahim da ake zargi da taimaka mata wajen aikata laifi tare da boye gaskiyar lamarin da bayar da bayanan karya kan dalilin rasuwar marigayi Nafi’u.

“Wadanda ake zargin sun yi karyar sanar da dangin Nafi’u kan dalilin rasuwarsa inda suka ce ya rasu ne saboda aikin basir da aka yi masa a asibiti,” in ji lauyan.