A ranar Juma’ar nan Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden, zai kai ziyarar aiki kasar Saudiyya, duk da irin caccakar da yake sha a kan hakan.
Biden na shan suka ne saboda a baya ya sha la’antar shugabannin Saudiyya gami da hana sayar wa kasar makamai, amma yanzu sai ga shi zai je kasarsu domin ganawa da kulla alaka da su.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 14,500 a shekara 4 A Afirka –ECOWAS
- An rantsar da shugaban rikon kasar Sri Lanka
Amma duk da sarkakiyar da ke tattare da ziyarar tasa, Mista Biden ya ce, “Tun ba yanzu ba, matsayina game da kare hakkin dan Adam ba boyayyen abu ba ne.
“Idan na hadu da shugabannin Saudiyya ranar Juma’a, hadafina zai kasance karfafa kawance ta yadda kowane bangare zai samu karuwa da kuma nauyi, ba tare da kau da kai daga mahangar Amurka ba.”
Ana kyautata zaton sha’anin tsaro da kasuwancin danyen mai su ne manyan batutuwan da za a fi mayar da hankali a tattaunawar ta Biden da Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman.
Sai dai kuma ana ganin ganawarsa da Yarima Mohammed bin Salman kadai ta isa abin magana, kuma za ta bude wani sabon babi a alakar kasashen biyu.
Idan ba a manta ba a baya shugaban na Amurka ya kira Saudiya zakka a cikin kasashe, saboda badakalar kisan gillar da aka yi wa fitaccen dan jaridar nan, Jamal Kashoggi a 2018.
A lokacin, Biden ya ce shi ba zai yi hulda da Mohammed bin Salman ba — saboda zargin da ake masa da hannu a kisan Kashoggi — sai dai mahaifin yariman, Sarki Salman.
Daga baya gwamnatinsa ta dakatar da sayar wa Saudiyya makamai da kuma tallafin da take bayarwa a yankin da rundunar kawancen kasashen Larabawa — wadda Saudiyya ke jagoranta — ke yi da ’yan tawayen Houthi a kasar Yemen.
Yanzu dai hankula sun koma sauraron jin ko shugaban na Amurka zai yi irin kalaman da ya yi a baya a ganawarsa da shugabannnin masarautar a ranar Juma’a.