A yau Lahadi ne Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tattaunawa ta bidiyo da ’yan wasan tawagar Najeriya ta Super Eagles gabanin karawar da za ta yi da Tunisia a gasar cin Kofin Afirka ta AFCON da ke gudana a Kamaru.
Cikin wani sako da Buhari ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bukaci ’yan wasan da su ci gaba da sanya farin ciki a zukatan ’yan Najeriya da cewa kada su tsaya a cin wannan wasa na yau kadai, su dauki kofin baki daya.
- AFCON 2021: Burkina Faso ta tsallaka mataki na gaba
- Shugaban Armenia, Armen Sarkissian ya yi murabus
Sai dai duk da wanna goyon baya da tawagar kwallon kafar ta samu daga jagoran kasar, bai hana tawagar ’yan wasan Tunisia ta fatattako ta daga gasar ba ma baki daya.
Ci daya mai ban haushi da tawagar Carthage Eagles ta Tunisia ta yi wa Super Eagles ta hannun Youssef Msakni a minti na 47 ne ya ba ta damar samun nasarar wucewa zagaye na gaba a gasar AFCON 2021.
Sai dai a yayin wasan, dan wasan Najeriya, Alex Iwobi mai buga tamaula a kungiyar Everton da ke buga gasar Firimiyar Ingila, ya karbi katin sallama bayan ketar da alkalin wasan ya yanke hukuncin cewa ya yi a daidai lokacin da bai wuce minti biyu ba da shigarsa wasan, bayan ya canji Kelechi Iheanacho a minti na 59.
Da wannan sakamako, Tunisia za ta fafata da tawagar The Stallions ta Burkina Faso a ranar Asabar, 29 ga watan Janairu wadda ita ma ta yi nasarar tsallakawa zuwa zagayen gab da na biyun karshe a gasar bayan ta kora tawagar Gabon gida a bugun fenareti.
Ana iya tuna cewa, Najeriya ce ta jagoranci rukuni na hudu da maki tara, yayin da Tunisia ta tsallake da kyar wadda aka yi gata bayan ta zo matsayi na uku da maki uku a rukuni na shida.
Kasashen biyu sun hadu a wasan neman na uku a gasar AFCON da aka fafata a kasar Masar a 2019, inda Najeriya ta yi nasara da ci 1-0.
Sau shida ke nan a tarihi Najeriya tana haduwa da Tunisia a gasar, kuma bata taba shan kaye ba sai a wannan karo da wasu ke ganin cewa Tunisian ta yi wa Najeriya abin da masu iya magana kan ce raina kama ka ga gayya.
A yanzu dai Tunisia ce za ta buga wasan Quater Final a Garoua tare da Burkina Faso ranar Asabar.