Rundunar tsaro ta ‘Operation Puff Adder II’ a Jihar Bayelsa ta cafke wani da ya kware wajen yin amfani da kakin soja don yi fashi da makami.
An dai kama wanda ake zargin ne da karamar bindiga kirar hannu a kan titin Ayama da ke Karamar Hukumar Yenagoa ta Jihar.
- Bidiyon Dala: Kotu ta umarci Ganduje ya biya Jaafar Jaafar N800,000
- Yaki da ta’addanci: Buhari na neman sojoji su canza salo
Kakakin ’yan sandan Jihar SP Asinim Butswat ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa a ranar Talata a birnin Yenagoa.
Ya ce “Yayin da rundunar ke sintiri akan titin Ayama, ta cafke wani dan fashi da karamar bindiga kirar hannu, a birnin Yenagoa.
“Bayan gudanar da bincike a gidansa, an sami harsasai da kakin soja ajiye a ciki.
“Ana ci gaba da tuhumarsa don samun wasu karin bayanan, kuma da zarar an kammala za a mika shi kotu,” a cewarsa.
Daga nan sai Kakakin ya shawarci al’ummar Jihar kan su ci gaba da taimakon jami’an tsaro da bayanan da zasu taimaka wajen bankado masu aikata laifuka.