Rundunar ’yan sandan Jihar Bayelsa ta cafke wani matashi mai shekara 29 a duniya da aiki a matsayin kwararren likita a Jihar Taraba.
Likitan bogin da ya shiga hannu ya bayyana cewar ya karancin Ilimin Halayyar dan Adam a Jami’ar Jihar Delta, kafin daga bisani ya shiga hannu a wani asibitin kudi.
- Mun gano Ministar da ta sayi kadarar Dala miliyan 37 a boye — EFCC
- Jerin wasannin farko na gasar Firimiyar Ingila a kaka mai zuwa
Wanda ake zargin ya ce, “Na hadu da mai takardun a hanyar Abuja mun dauki hotuna tare, a lokacin da yake kokarin tura min hotunan ne ya hada min da hoton takardunsa,” daga nan ya fara ungulu da kan zabo a matsayin likita.
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Asinim Butswat, ta shaida wa manema labarai cewar an kai musu karar wanda ake zargin kan kwarewarsa a matsayin kwararren likita.
Da yake nasa jawabin bayan cafke likitan bogin, Shugaban Kungiyar Likitoci (NMA) reshen jihar, Ngowari Torunana, ya ce ce sun bincika tare da gano likitan na bogi ba shi da wata cikakkiyar kwarewa a kan aikin.
Bayan jami’an tsaro sun titsiye shi, wanda ake zargin ya amsa cewar takardun da yake amfani da su ba nasa ba ne.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bayelsa, Mike Okoli, ya ce likitan bogin ya jima yana neman aiki tsakanin Jihar Delta da Jihar Bayelsa.