✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dubban mutane sun yi zanga-zanga kan mallakar bindiga a Amurka

Dubban mutane wadanda galibinsu matasa ne kuma dalibai suka yi gangami a birnin Washington da ke Amurka domin gudanar da zanga-zangar neman ganin an samar…

Dubban mutane wadanda galibinsu matasa ne kuma dalibai suka yi gangami a birnin Washington da ke Amurka domin gudanar da zanga-zangar neman ganin an samar da dokar da za ta hana mallakar bindiga barkatai.

Wannan bukatar ta biyo bayan wani hari ne da aka kai a wata makaranta da ke Jihar Florida inda wani matashi ya shiga makarantar da ake kira Marjory Stoneman Douglas High School, ya harbe mutum 17.

daya daga cikin daliban da suka yi fice a kan neman a samar da  dokar  mai suna Emma Gonzales ta shaida wa dubban jama’ar da suka yi cincirindo a gangamin cewa babbar kawarta na cikin wadanda  suka  rasa ransu sakamakon wannan hari kuma  burinta shi ne ta ga cewa an samar da canji game da  dokar.

A ca birnin Atlanta da ke Jihar Geogia ma an gudanar da irin wannan gangami domin daliban makarantar da aka kashe.

Cikin sanannun mutanen da suka halarci zanga-zangar a Atlanta har da sanannen dan Majalisar wakilan nan mai fafutikar kare hakkin bil Adama, John Lewis.

Magajiyar Garin Atlanta, Misis Keisha Lance ita da wadansu ’yan Majalisar Dokokin Jihar Atlanta sun halarci gangamin.

Haka a birnin New York, dubban jama’a ne suka yi dafifi a wajen irin wannan gangami. 

Tsohon makadin nan da yayi fice Paul McCarthy ya bi sahun wadanda suka halarci gangamin, kuma ya shaida wa manema labarai cewa a daidai wurin da ake wannan gangami a New York ne aka kashe abokinsa da suke kida tare mai suna John Lema, kuma ta irin wannan hanya ce ta mallakar bindiga barkatai.

Wadanda suka shirya gangamin dai sun ce an yi irinsa har 800 a duk fadin Amurka da duniya baki daya, ciki har da biranen Tokyo da Berlin da Paris, inda Amurkawa suke da yawa kuma sun fito kwansu da kwarkwata domin nuna goyon bayansu ga ’yan uwansu da ke gida Amurka.

Sai dai a cikin Amurka masu wannan zanga-zangar sun samu cikas.

Wani mai suna Joe da jaridar Aminiya ta tattauna da shi game da gangamin cewa ya yi wannan abu yana sosa rai.

Shi kuma Sanata Marco Rubio wanda a mazabarsa ne makarantar da aka yi harbin na baya-bayan nan take, ya sha suka daga daliban makarantar domin ya karbi gudunmawar kudi har Dala miliyan 3 daga kungiyar masu sayar da bindiga, Kuma baya ga wannan, kafin ranar da za a gudanar da gangamin, Sanatan ya fitar da sanarwar cewa yana goyon bayan  zanga-zangar, amma wajibi ne a cimma matsaya domin ba kowa ne yake goyon bayan bukatar ba.

Sai dai har aka yi gangamin aka kare, Shugaban Amurka Donald Trump bai ce uffan ba.

Dubban masu gangamin sun yi cincirindo a bakin titi da jerin motocin Trump suka saba wucewa zuwa wurin hutawarsa, amma a wannan karon ya bi ta wata hanya domin kauce wa masu zanga-zangar.

Mai magana da yawun fadar gwamnatin Amurka, Lindsay Walter a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce “Muna yaba wa matasan Amurka da suka shirya wannan gangami domin neman ’yancinsu..” Sanarwar  ta ci gaba da cewa kare yara shi ne babban burin Shugaban Amurka, inda ta ce wannan ne ma ya sa ya bukaci majalisun kasar su samar da dokar da za ta hana samun tashin hankali a makarantu.