✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

DSS ta tsananta binciken Emefiele kan daukar nauyin ta’addanci

Ana zargin Gwmanan CBN da daukar nauyin haramtacciyar kungiyar IPOB da kuma karkatar da kudaden gwamnati

Hukumar tsaro ta DSS ta tsananta bincike a kan Gwmanan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, domin gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin almundahana da kuma daukar nauyin kungiyar ta’addanci ta IPOB.

DSS tana kuma zargin Mista Emefiele da damfara da kuma amfani da shirye-shiryen tallafin CBN wajen azurta kansa, karkatar da kudaden gwamnati da kuma yi mata zagon kasa.

Aminiya ta gano haka ne a yayin da wasu rahotanni ke zargin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya da bai wa Emefiele kariya a gida da kuma ofishinsa, domin hana a kama shi, zargin da Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta musanta.

Bayan yunkurin DSS na tsare Gwamnan CBN din a baya ya faskara, hukumar ta bi wasu sabbin hanyoyi tare da tsananta bincike a kansa kan zage-zagen da ake masa.

A baya-bayan nan kafar yada labarai ta Premium Times ta wallafa wasu bayanai na musamman da ta samu daga kotu kan zarge-zargen da Emefiele ke fuskanta.

Takardar kotun ta nuna ana zargin Gwmanan CBN din da daukar nauyin ’yan bindiga da kuma ayyukan kungiyar ta’addanci ta IPOB.

Rahoton ya kuma zargi Emefiele da yin zagon kasa ga Gwamnatin Shugaba Buhari, daukar nauyin ta’addanci da kuma wasu abubuwa da ke barazana ga tsaron Najeriya.

Ana kuma zargin sa da facaka da kudaden Bankin NIRSAL da kuma kudaden shirin tallafin noma na Anchor Borrower wadanda CBN ke kula da su.

Yadda Emefiele ke daukar nauyin IPOB

Ana zargin Gwmanan na CBN ne da daukar nauyin reshen soji na kungiyar IPOB, wato ESN, ta hanyar amfani da kudaden sata da kuma wadanda ya yi amfani da su wajen neman takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC mai mulki, wanda Bola Tinubu ya lashe zaben fidda gwanin.

Gwamnatin Tarayya ta jima da ayyana IPOB a matsayin Kungiyar ta’addanci.

IPOB dai kungiya ce da ke neman ballewa daga Najeriya, kuma ta dade tana kai miyagun hare-hare a kan cibiyoyin gwamnati da na hukumomin tsaro tare da kashe mutane, musamman jami’an tsaro.

Maharan IPOB sun kuma kashe faraten hula da dama, tare da tilasta wa mazauna yankunan Kudu maso Gabashin Najeriya zaman gida a ranakun Litinin.

A baya-bayan nan dai IPOB ta tsananta kai hare-hare a kan ofisoshin ’yan sanda, inda take kashe jami’ai ta sace makamai, sai kuma ofisoshin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), inda suke kona kayayyakin zabe.

Dambarwar Emefiele

Yunkurin Aminiya na jin ta bakin Emefiele ko ofishinsa ya ci tura.

Takarar shugaban kasa

Idan ba a manta ba, tun lokacin da Emefiele ya bayyana aniyarsa ta neman takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC ake ta ce-ce-ku-ce a kansa.

’Yan Najeriya sun kalubalance shi a lokacin bayan ya sayi fom din neman takarar shugaban kasa a APC a kan Naira miliyan 100, amma ya bayyana cewa masoyansa ne suka saya masa.

Daga bisani, bayan an nemi ya yi murabus daga matsayinsa, ya je kotu, ta kuma ba shi izinin tsayawar takara.

Sauyin kudi

Sai dai bai yi nasara ba a zaben takara, wanda daga bisani ya ci ga da aikinsa a CBN, wanda shi ma ya tayar da kura.

Daga bisani, bayan sanar da sauyin takardun Naira 200, 500 da 1,000 da kuma tsarin takaita amfani da tsabar kudi da CBN ya yi Emefiele ya sake dawowa bakin ’yan Najeriya.

A kwanakin baya, dan Majalisar Wakilai ya zargi Emefiele da karkatar da wasu kudade da yawansu ya kai Naira tiriliyan 80, zargin da Gwamnan bankin ya karyata.

Tun farkon bullo da batun sauyin kudi, Ministar Kudi da Tsare-tsare ta ce ma’aikatarta ba ta da masaniya a kan lamarin.

Ta kuma yi gargadi cewa matakin zai kawo matsalar tattalin arziki.

Canjin Kudi: Majalisa ta gayyaci Emefiele

’Yan Najeriya sun yi ta korafi kan batun, lamarin da ya sa Majalisa ta bukaci Emefiele ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi.

Sau biyu majalisa na gayyatar sa ba tare da ya hallara.

Da farko ya aike wa kwamitin majalisar cewa ya yi tafiya kasar waje domin aiki, wanda ya sa aka dage zaman, inda a karo na biyu ya turo wakiliyarsa bisa uzurin cewa yana duba lafiyarsa a kasar waje.

Sai daga bisani, ya dawo suka gana, kurar ta dan lafa, amma duk da haka ’yan majalisar ba su yarda ba, inda suka bukaci karin lokacin sauyin kudin.

Babu labari mai dadi

Ana gab da cikar wa’adin ranar 31 ga watan Janairu da CBN ya bayar na daina amfani da tsoffin takardun kudin da aka sauya, aka yi ta ji-ta-ji-tar cewa za a kara lokaci.

Ana tsaka da haka ne Emefiele, bayan wata ganawa da ya yi da Buhari, ya sanar cewa ba za a kara lokacin ba.

Bayan an yi ta kai ruwa rana, a ranar 30 ga watan Janairu, Emefiele ya sanar cewa Shugaba Buhari ya kara wa’adin da kwana 10, zuwa 10 ga watan Fabrairu.

Idan mai karatu zai tuna, tun a jajibirin fara aikin dokar sabbin takardun kudin suka gagari ’yan Najeriya samu, sai sun je banki, ga shi kuma sabbin kudin ba sa samuwa.

Lamarin da ha haifar dogayen layuka da guna-guni daga ’yan Najeriya, musamman ganin cewa a wasu bankunan, abin ake ba su bai wuce N3,000 ba na sabbin kudin.

Kotun Koli

Bayan cikar wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu, da rashin nasarar gwamnonin APC wajen ganin Shugaba Buhari ya kara wa’adin, wasu daga cikinsu suka maka CBN da Gwamnatin Tarayya a gaban Kotun Koli suna neman ta dakatar da haramcin tsoffin takardun kudin.

Kotun ta ba da umarnin wucin gadi bisa bukatar gwamnonin sannan ta dage zaman.

Gwamnonin sun dauki matakin ne bayan Buhari ya ce su ba shi kwana bakwai zai yi tunani, yana mai jaddada cewa CBN ya ba shi tabbacin zai wadatar da ’yan kasa da sabbin kudaden.

Daga bisani Majalisar Koli ta Kasa ta yi zaman inda ta gayyaci Emefiele, ta umarci CBN ya samar da sabbin takardun kudin a wadace, ko kuma a ci gaba da amfani da tsoffin.

Bayan nan ne Koun Koli ta umarci jihohi 12 da suka shigar da kara gabanta su hade karar a wuri daya da kuma bangaren da ake kara a gefe guda, sannan a dage sharia’r zuwa ranar 22 ga watan Fabrairu.

CBN ya lashe amansa

Daga bisani ne Buhari ya ba da umarnin ci gaba da amfani da tsohuwar takardar N200 zuwa ranar 10 ga watan Afrilu, tsohuwar N500 da N1,000 sun daina aiki, amma masu su na iya kaiwa CBN a tura zuwa asusun bankinsu.

Washe garin fara hakan, bayan ’yan Najeriya sun yi cikar kwari a rassan CBN d ake jihohi, babban bankin ya fitar da sanarwa cewa masu tsoffin kudin da ba su wuce N500,000 ba su kai wa bankunan kasuwanci, wadanda ke da sama da N500,000 kuma su kai ofisoshinsa.

Cikin dan lokaci bayan fitar sanarwar da CBN ya aike wa bankunan kasuwanci, ya lashe amansa, yana mai karyata sanarwarsa ta farko.

Duk da haka a halin da ake ciki, wasu bankunan kasuwanci sun ci gaba da karbar tsoffin takardun kudin daga hannun jama’a.