Sakamakon sanarwar tsaro da Ofishin Jakadancin Amurka da ke Najeriya ya yi wa ’yan kasar kan shirin da ’yan ta’adda da kai hari a Abuja, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ta yi kira ga ’yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu tare daukar matakan kariya.
Ofishin jakadancin Amurka ya bayar da sanarwar tsaro ga ’yan Amurka a ranar Lahadi, inda ya yi nuni da cewa akwai shirin kai hare-hare a wuraren tarukan jama’a da cibiyoyin gwamnati a Abuja.
- Yadda ISWAP ta yi wa ’yan Boko Haram yankan rago
- NAJERIYA A YAU: Kudurin dokar hukunta ’yam madigo da luwadi a kasar Nijar
A sanarwar an bayyana cewa: “Akwai barazanar kai hare-haren ta’addanci a Najeriya, musamman a Abuja.
“Ba a tantance ina da ina za a iya kai harin ba, amma dai akwai yiwuwar kai hare-hare kan gine-ginen gwamnati, wuraren ibada, makarantu, kasuwanni, manyan shaguna saye-saye, otal-otal, mashaya, gidajen cin abinci, wuraren wasannin motsa jiki, tashoshin mota da sauransu.
“Matakan da ya kamata a dauka: A guji yin duk wata tafiya ko zuwa wani waje da bai zama dole ba, a kasance cikin shirin ko-ta kwana, a guji shiga taron jama’a, sannan saboda tsaro, kowa ya tabbata yana da isasshen caji a waya saboda tsaro.”
Sai dai a martanin da hukumar DSS ta fitar ta bakin kakakinta, Peter Afunanya, ya ce sanarwar ta yi kama da wadda hukumar ta taba fitarwa a kwanan nan.
DSS ta ce: “Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sha aike mana da shawarwari kan hare-hare a Abuja; Amma idan jama’a za su iya tunawa DSS ta yi irin wannan gargadi daban-daban a baya.
“Ana shawartar jama’a da su kasance cikin shiri sannan su taimaka wa jami’an tsaro da bayanai ta yadda za a samu nasarar kama duk wani wanda ke shirin aikata ayyukan ta’adanci.
“A halin da ake ciki, hukumar ta yi kira da a kwantar da hankali yayin da take aiki tare da sauran jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki don wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Abuja da kasa baki daya.”