Hukumar tsaro ta DSS ta kama wani mutum da aka gano yana jagorantar wata ƙungiya mai zaman kanta mara rajista a yankin Neja Delta.
Mista Kennedy Tabukoi, ya shiga hannu ne kan amfani da kungiyar bunƙasa yankin Neja Delta (NDDI), wajen yi wa wasu manyan mutane da jami’an gwamnati zagon ƙasa.
Wani jami’in DSS da ya shaida mana cewa an damƙe Tabukoi ya bayyana cewa hukumar ta gano cewa wanda ake zargin na da hannu wajen kista wasu zanga-zangar fafutikar adawa da gwamnati a yankin Neja Delta.
“Duk lokacin da jami’an gwamnati suka ki biya masa buƙata sai ya tunzura wasu kungiyoyi su yi bore da tattakin adawa da su.”
- Sojojin Nijeriya sun kora Lakurawa zuwa Nijar
- An kama Akol Koor tsohon shugaban hukumar leken asirin Sudan ta Kudu
Ya ce, jami’an tsaro sun daɗe suna neman Mista Tabukoi, bayan wasu jami’an gwamnati sun kai ƙara kan yadda yake musu barazana idan ba su ba shi wasu maƙudan kuɗaɗe ba.”
A ranar Alhamis Mista Tabukoi ya jagoranci wata zanga-zangar ƙungiyoyin yankin Neja Delta a kofar Majalisar Dokoki ta Ƙasa kan zargin rufa-rufa a ɓangaren man fetur.
Tabukoi na zargin ’yan majalisar dokokin ta ƙasa da yunƙurin daƙile bincike a ɓangaren man fetur.