Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS ta cafke malamin nan Baffa Hotoro da abokinsa, Habib Haroun wanda aka fi sani da Abu Aaman, bisa zarginsu da munana ladabi ga Manzon Tsira Annabi Muhammad (S.A.W).
Ma’aikatar Harkokin Addinai ta Kano ce ta bayyana hakan a Asabar din nan, inda ta ce za a yi bincike sannan a dauki matakin da ya dace a kansu.
- Diket Plang ya lashe kujerar Sanatan Filato ta Tsakiya
- INEC ta hana ’yan jarida shiga cibiyar tattara sakamakon zabe a Adamawa
Kwamishinan Harkokin Addinai na Jihar Kano, Ustaz Muhammad Nazifi Bichi ya yi wa Aminiya karin haske cewa sun karbi korafe-korafe akan kalaman batanci da matasan malaman ke yi, lamarin da suka sanar wa Hukumar DSS don daukar matakin da ya dace.
A cewarsa, “a yanzu haka suna hannunta Hukumar DSS, inda take gudanar da bincike akan lamarin da zarar ta kammala bincike, an kuma same su da laifi to za a gurfanar da su gaban kuliya don fuskantar hukunci.
Sai dai Hukumar ta DSS ta bakin Daraktanta na Kano, Alhassan Muhammad ya bayyana cewa sun gayyaci malamin ne ba wai kama shi suka yi ba kamar yadda mutane ke yadawa.
“A gaskiya gayyatar sa muka yi wanda kuma yake da alaka da irin kalaman da suke yi a karatuttukansu wanda kuma ake ganin suna taba akidun wasu mutane a Kano.
“Mu kuma jihar ce a gabanmu don haka muke kokarin ganin cewa an sami zaman lafiya a jihar.
A cewar Daraktan, sun lura cewa rayuwar malaman ma tana cikin hatsari don haka ya zama dole su shiga cikin lamarin.
Tun dai a kwanaki baya ne Baffa Hotoro ya goyi bayan Malamin nan, Dokta Dustin Tashi na Jihar Bauchi da ake zargi da yin batanci ga Annabi (SAW).
Baffa Hotoro ya ce kalaman malamin suna kan daidai har ma ya kara da wasu kalaman batanci akai, lamarin da ya janyo al’ummar jihar suka rubuta takardun korafi a kan malamin tare da neman hukumomi su shiga cikin lamarin.