✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

DSS ta gano sabuwar dabarar fashi da makami a Kano

An kama su yayin da suke kokarin tserewa daga wurin da suka aikata laifin.

Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya (DSS), ta yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su kasance masu lura a yayin da suke yawo da kudi ganin cewa wasu gungun masu fashi da makami sun bullo da sabuwar dabarar kwacen dukiyar jama’a birnin na Dabo.

Darektan Hukumar DSS na Jihar Kano, Alhassan Muhammad ne ya yi wannan kira a ranar Juma’a ya yi holen wasu mutum uku daga cikin gungun yan fanshin ga manema labarai.

A cewarsa, an kama ababen zargin ne bayan sun yi wa wani mutum fashi da makami na dukiyarsa.

Ya ce ta’adar fashi da makami na kara tsananta la’akari da yadda Hukumar ke karbar korafe-korafen mazauna da lamarin ya shafa.

Da yake zayyana yadda masu fashi da makamin ke gudanar da ayyukansu, Darektan ya ce baya ga Jihar Kano, suna kuma aiwatar da wannan mummunar ta’ada a Jihohin Kaduna Katsina, Jigawa, da kuma Borno.

Ya ce wannan gungun miyagu a kullum sukan yi shawagi a kusa da Bankuna tun daga karfe 9 na safe zuwa 4 na yamma domin su tantance mutanen da ke shiga bankunan karbo kudi sannan su bi sahunsu har wurin da za su samu damar kwace kudin.

Da yake jawabi dangane da yadda ababen zargin suka shiga hannu, Darektan ya ce an kama su ne a ranar 2 ga watan Nuwamba bayan sun karbe Naira 500,000 daga hannun wani mutum da ya fito daga banki.

Ya ce jami’ansu ne suka yi ram da su yayin da suke kokarin tserewa daga wurin da suka aikata laifin.

Kazalika, ya ce ababen zargin sun taba aikata makamancin wannan laifi yayin da aka sami wasu motoci guda biyu da kudaden sata a hannunsu.

Ya ce za a mika su ga hannun jami’an ’yan sanda domin su ci gaba da gudanar da bincike.