✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta cafke Doyin Okupe a hanyar zuwa Landan

DSS na neman ba'asin hanyar da ya bi na biyan tarar da kotu ta yanka masa.

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama tsohon Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zaben dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP, Doyin Okupe.

A cewar lauyansa Tolu Babaleye, an kama dan siyasar ne a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Ikeja a Jihar Legas, a lokacin da yake shirin tafiya Landan.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, ta samu Okupe, mai bai wa tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan shawara kan Harkokin Jama’a, da laifin karkatar da kudaden makamai daga Ofishin tsohon mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro.

Mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta bayyana cewa, masu tuhuma sun gabatar da karar satar kudi a kan Okupe wanda aka ci shi tarar Naira miliyan 13.

A shekarar 2019, Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arziki Zangon Kasa (EFCC), ta tuhumi Okupe da laifuka 59 ciki har da wadanda suka shafi karkatar da kudi har Naira miliyan 240 daga hannun Sambo Dasuki.

An gurfanar da shi tare da wasu kamfanoni biyu – Value Trust Investment Ltd da Abrahams Telecoms Ltd.

Mai shari’a Ojukwu, ta samu Okupe da laifuka 26 daga cikin tuhume-tuhume 59 da EFCC ta gabatar a kansa.

Alkalin ya yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu kan kowanne laifi daga cikin tuhume-tuhumen 26 ko kuma zabin biyan tarar N500,000 a kan kowanne laifin.

Alkalin ta kuma bayar da umarnin cewa idan ba a biya tarar cikin sa’o’i 24 ba, za a tisa keyar Okupe zuwa gidan yari, lamarin da ya yi gaggawar cika wa’adin saboda gudun zaman wakafi.

A cewar Babaleye, DSS ta bukaci Okupe ya gabatar da hanyoyin da ya bi wajen biyan tarar kudaden da kotun ta yanka masa.

Har yanzu dai hukumar DSS ba ta ce komai kan ikirarin lauyan nasa ba.

Okupe dai ya ajiye mukaminsa na shugabancin yakin neman zaben Peter Obi bayan da aka yanke masa hukunci, inda hadimin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, Akin Osuntokun ya maye gurbinsa.